Buhari ya gana da bakar fata da aka zaba Sanata a karo na farko a Italy

Buhari ya gana da bakar fata da aka zaba Sanata a karo na farko a Italy

- Shugaba Buhari ya hadu da, Toni Iwobi, bakar fata na farko da aka zaba a matsayin Sanata a kasar Italy

- An haifi Mr Iwobi ne a Najeriya amma ya kwashe shekaru 41 yana zama a kasar ta Italy

- Mr Iwobi da sauran tawagar Sanatocin Italy sun tattauna wasu matsalolin da ke fuskantar Afirka tare da alkawarin kawo ziyara Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Mr Toni Iwobi, bakar fata na farko kuma haifafen Najeriya da aka zaba a matsayin Sanata a kasar Italy.

Mr Iwobi wanda ya zauna a Italy har na shekaru 41 ya jagoranci tawagar Sanatocin Italy ne zuwa wani taro da shugaba Muhammadu Buhari a yayin da shugaban kasar ya ziyarci birninNew York da ke Amurka domin hallartar taron majalisar dinkin duniya karo ne 73.

Shugaba Buhari ya gana da bakar fata na farko da ya zama Sanata a Italy
Shugaba Buhari ya gana da bakar fata na farko da ya zama Sanata a Italy
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Fitar da 'yan takara: APC ta nada gwamnoni a matsayin jami'an zabe

Shugaba Buhari ya taya Iwobi murna kan zabensa da akayi a matsayin Sanata a watan Maris na 2018 a karkashin jam'iyyar League Party tare da cewa zabensa ya nuna cewa mutanen kasar Italy suna mutunta al'umma duk da banbancin launin fata.

Tawagar da Italy sun tattauna abubuwa da dama ciki har da matsalar bakin haure daga Afirka da yadda za'a magance matsalar ta hanyar saka jari a Afirka da kuma batun habbaka tafkin Chadi ta hanyar kwararo ruwa da daga wasu tekun kasashen waje.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce abubuwan da ke sanya 'yan Afirka hijira zuwa kasashen turai sun hada da rashin tsaro, rashin ilimi, rashin ingantaccen asibitoci da sauransu. Ya kuma kara da cewa dumaman yanayi yana kawo cikas ga babban kasa kamar Najeriya.

Tawagar majalisar ta kasar Italy ta ce za ta ziyarci Najeriya nan ba da dadewa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel