Musulmai ma fuskantar tsangwama, kyara da cin fuska a nahiyar turai – Bincike

Musulmai ma fuskantar tsangwama, kyara da cin fuska a nahiyar turai – Bincike

Masana da shuwagabannin tsara dokoki a nahiyar turai sun hadu a wani babban taro a majalisar dokokin nahiyar turai dake Brussel a ranar Laraba 26 ga watan Satumba don tattauna hanyoyin shawon kana matsalar cin zarafi tare da tsangwamar musulmai a yankin.

KU KARANTA: Ma’aikata a jahar Kaduna sun yi fatali da batun shiga yajin aikin kungiyar kwadago

A yayin taron an gabatar da wani rahoton wani bincike da aka gudanar a kasashen nahiyar turai guda takwas daga ciki harda kasar Faransa, Birtaniya da Jamus, inda rahoton ya nuna ana samun karuwar nuna tangwama ga Musulmai a turai.

Musulmai ma fuskantar tsangwama, kyara da cin fuska a nahiyar turai – Bincike
Musulmai
Asali: Facebook

“Wannan matsalar na gurbata zamantakewarmu a turai tare da sanya gaba a tsakaninmu” Inji wani dna majalisar dokokin nahiyar Turai dake wakiltar birnin Landan Jean Lambert, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Karin tsangwama ga musulmai ya danganta ne da maganganun da kafafen sadarwar ke yi dake rura matsalar tare da zantuttukan yan siyasa, dukkaninsu na kara ma turawa kwarin gwiwar kin jinin musulmai a yankunansu.” InJi rahoto.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata masaniya mai suna Amina Easat-Daas dake aikin wayar da kan turawa game da illar nuna tsangwama da wariya ga Musulmai tana cewa “Bincikennan ya nuna yaduwar tsangwama ga Musulmai, tare da yadda ya shiga duka fannonin rayuwa da zamantakewa,

“Kokarinmu shine mu kawar da wannan matsalar ta hanyar wayar da kawunan mutanenmu tare da bayyana musu kyawawan halayen musulmai, zaman lafiyarsu tare da gagaruman gudumuwar da musulmai ke bayarwa a wajen inganta kasashenmu.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng