Buhari yace shi kadai ke neman kujerar Shugaban kasa a APC

Buhari yace shi kadai ke neman kujerar Shugaban kasa a APC

- Buhari yace shi kadai zai rikewa Jam’iyyar APC tuta a zaben 2019

- Shugaban kasar yace ya kuma shirya karawa da masu neman takara

Buhari yace shi kadai ke neman kujerar Shugaban kasa a APC
Shugaba Buhari yace shi kadai ne 'Dan takarar APC a 2019
Asali: Depositphotos

Labari ya zo mana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa shi kadai ne ke neman takarar kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar sa ta APC mai mulki a zabe mai zuwa na 2019.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda yanzu haka yana Kasar Amurka inda yake halartar wani muhimmin taro na Majalisar dinkin Duniya ya bayyana cewa shi kadai ne ‘Dan takarar Jam’iyyar APC a zaben 2019.

Buhari ya fadawa Mutanen Najeriya da ke zaune a Kasar Amurka cewa kafin yanzu akwai wadanda su ke sha’awar kujerar a Jam’iyyar APC, yace amma yanzu duk sun sauya sheka domin su gwabza da shi a zaben badi.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC tayi nasara bayan an karasa zaben Jihar Osun

Shugaban kasar yace wanda su ke neman takarar Shugaban kasar sun koma wasu Jam’iyyu inda su ke sa ran su yi takara da shi. Buhari ya bayyana cewa a shirya yake ya kara da wadanda su ke ganin cin tan a zaben na 2019.

Har wa yau, Shugaba Buhari ya fadawa mutanen Najeriya da ke waje cewa su san da cewa duk da yana Shugaban kasa, kuri’a guda tal yake da ita don haka yayi kira da su dawo gida su yi zabe inda yace za ayi zaben kwarai na gaskiya.

Daga cikin wadanda su ka bar APC domin su nemi takarar Shugaban kasa akwai tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Shugaban Majalisa Bukola Saraki da Rabiu Kwankwaso da kuma Aminu Tambuwal.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel