Kiris ya rage a hallaka tsohon hadimin Sarkin Kano

Kiris ya rage a hallaka tsohon hadimin Sarkin Kano

- Tsohon sakataren Sarki Ado Bayero ya tsallake rijiya da baya

- Mazaje biyar tare da makaman su suka tsinkaye shi har cikin gidan shi

- 'Raina suka zo nema'

Kiris ya rage a hallaka tsohon hadimin Sarkin Kano Lamido Sanusi
Kiris ya rage a hallaka tsohon hadimin Sarkin Kano Lamido Sanusi
Asali: UGC

Tsohon sakataren Sarki Ado Bayero wanda sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya kora, Isa Sanusi Bayero, ya tsallake yunkurin kisa a ranar asabar a gidansa dake sharada, a Kano.

Makasan dauke da makamai su biyar ne suka tsinkaye shi har gidan shi da misalin karfe 7:40 na dare domin zaqulo shi.

Isa Sanusi wanda akafi sani da Isa Pilot, yace da misalin karfe 7:40 na yamma ne yaji karar bindiga amma sai yayi tunanin fashewar taya ce.

"Direba na ya fita yaga me ke faruwa, sai kawai makasan suka taso shi gaba da bindigogi suna tambayar inda nake. Da naji surutai a waje, sai na like ta kofa. Karar kofar ta sa suka maido hankalin su gurina, ni kuwa sai na rufe ta kofar da sauri tare da kashe wuta. Wannan ya basu tsoro suka gudu".

DUBA WANNAN: A kula da yaduwar makaman Nukiliya - Buhari ga Duniya

Direban kuwa yace sun tasa shi gaba ne sai ya nuna musu inda ubangidan nashi yake. Inda yace musu shima bako ne, kuma bai San wani Isah ba.

"Amma kafin su tafi, sai daya yace su kashe koda mutum daya ne don su bar sako. Shugaban su sai yace ai Isah Pilot kadai aka sa mu kashewa." inji Direban.

"Bayan nan ne Yan sanda suka zo gidana don tsaro tare da yin tsatsauran bincike akan matsalar" Isah Pilot ya fada.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel