KARIN BAYANI: Yadda APC ta samu nasara a kananan hukumomi 3 cikin hudu na zaben jihar Osun

KARIN BAYANI: Yadda APC ta samu nasara a kananan hukumomi 3 cikin hudu na zaben jihar Osun

Gboyega Oyetola, dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar APC a zaben ranar Alhamis da ake kan gudanarwa zagaye na biyu, ya baiwa takwaransa na jam'iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke tazara mai nisa, inda ya lashe kuri'un kananan hukumomi 4 cikin 3 da ake gudanar da zaben.

Oyetola ya samu nasara a akwatuna biyu da ke Ile Ife ta Kudu, inda ya samu kuri'u 283, yayinda Ademola Adeleke, ya samu kuri'u 15. A karamar hukumar Ife ta Arewa kuwa APC ta samu kuri'u 126, yayin da Adeleke ya tashi da kuri'u biyu kacal.

A dukkanin akwatunan zaben, an nemi jami'an sa ido na jam'iyyar PDP an rasa su ko sama ko kasa.

KARANTA WANNAN:

KARIN BAYANI: APC ta samu nasara a kananan hukumomi 3 cikin hudu na zaben jihar Osun
KARIN BAYANI: APC ta samu nasara a kananan hukumomi 3 cikin hudu na zaben jihar Osun
Asali: Original

Sakamakon zaben gunduma ta 5 a akwati na 7 na garin Alekuwodo da ke karamar hukumar Osogbo, APC ta samu kuri'u 299 yayinda PDP ta tashi da 165.

Dan takarar kujerar gwamnan karkashin PDP, ya samu nasarar zuwa zaben zagaye na biyu da kuri'u 353 akan APC, sai dai daga alamu reshe ya juye da mujiya, don kuwa APC ta baiwa PDP tazara mai nisan gaske a kananan hukumomin 3 cikin 4 da ake gudanar da zaben.

Ana gudanar da zaben raba gardamar ne a mazabu 7 dake kananan hukumomin jihar Osun 4.

Ga jerin sakamakon kamar yadda suke a mazabun da aka gudanar da zaben

Orolu, mazaba ta 8, akwatu ta 4

APC 198 PDP 15

Orolu, mazaba ta 9, akwatu 3

PDP 64

APC 41

Karamar hukumar Ife ta kudu, akwatu ta 012

Adadin masu kada kuri’a da aka tantance 310

Kuri’ar da ta lalace 6

APC 283

APA 3

APGA 1

PDP 15

SDP 1

UPN 1

Mazaba ta 10, akwatu ta 02, karamar hukumar Ife ta arewa

APC 126

PDP 2

Mazaba ta 8, akwatu ta 10, karamar hukumar Ife ta kudu

APC 172

PDP 21

Mazaba ta 5, akwatu ta 17, karamar hukumar Osogbo

APC 299

PDP 165

Ife ta Arewa

APC 132

PDP 02

Zamu cigaba da kawo karin sakamkon zaben da zarar sun shigo hannu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel