Giwa ta kashe wata da ta dauki hoton ta

Giwa ta kashe wata da ta dauki hoton ta

- Giwa ta kashe wata mata a wani gidan namun daji da ke kasar Zimbabwe

- Matar 'yar kasar Jamus mai shekaru 49 ta matsa kusa da giwayen ne domin daukansu hoto amma suka kai mata hari

- Jami'an da ke kula da dabobin gandun dajin sun ce ba su san tabbacin abinda ya harzaka giwayen ba

Wata giwa ta kashe wata mata 'yar kasar Jamus mai shekara 49 a wani shahararren wurin ajiye namun daji a Zimbabwe a bayan ta dauki giwayen hoto kamar yadda jami'i mai kula da namun dajin bayyana.

Ma'aikatan wurin ajiye namun dajin sun ce giwayen sun kaiwa matar hari ne a Mana Pool a farkon wannan makon kuma daga baya ta rasu a ranar Laraba sakamakon raunin da gwiwar ta yi mata.

Giwa ta kashe wata da ta dauki hoton ta
Giwa ta kashe wata da ta dauki hoton ta
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yaki da rashawa: Magu ya yiwa 'barayin gwamnati' sabuwar albishir

Matar tana tare da wasu gungun 'yan yawon bude idanu ne lokacin da ta hango giwayen, inji Tinashe Farawa, Mai magana da yawun hukumar Zimbabwe Parks da hukumar kula da namun daji.

Ya ce ta fito daga motar da suke cikin domin ta dauki hoton giwayen a kusa da su sai dai bai san ko hakan shi ne ya bata wa giwayen rai ba.

"Ba mu san tabbacin abinda ya saka giwayen suka harzaka ba har suka kaiwa matar hari," inji Mr Farawo.

Ya cigaba da cewa, dama ana gargadin masu ziyara ko yawon bude idanu su rika nesa da dabobin dajin duk lokacin da suka zo yawon bude idanu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel