Za a zabi shugaba Buhari a 2019 ko don ayyukan da ya shimfida a kasar - Goni

Za a zabi shugaba Buhari a 2019 ko don ayyukan da ya shimfida a kasar - Goni

- Shugabar kungiyar GMBO, Dr. Fatima Mohammed Goni, ta ce akwai dalilai 150 da za su sa a sake zabar Buhari a 2019

- A cewar ta, ayyukan da shugaban kasar ya samu nasarar kammala a cikin shekaru 3 sun isa Buhari ya zarce

- Ta ce ya kamata a duba batun yawan 'yan takarar kujerar gwamamnan jihar Borno karkashin jam'iyyar APC

Shugabar kungiyar yakin zaben Buhari daga matakin farko GMBO, Dr. Fatima Mohammed Goni, ta ce kungiyar na da dalilai 150 da suka bada tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci ya zarce a babban zaben 2019 da ke tahowa.

A cewar ta, ayyukan da shugaban kasar ya samu nasarar kammala a cikin shekaru 3 wadanda suka shafi bangaren tattalin arziki, gina kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa sun isa Buhari ya koma ofishinsa a karo na biyu.

Goni, a lokacin da ta ke zantawa da manema labarai a sakatariyar kungiyar da ke Abuja, ta ce idan aka cire 'yancin da doka ta baiwa shugaban kasar na sake tsayawa takara, ayyukan da ya shimfida a bayyane suke ga kowane dan Nigeria ya gani kuma ya taba.

KARANTA WANNAN: Dakile ta'addanci: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a jihar Kwara

Za a zabi shugaba Buhari a 2019 ko don ayyukan da ya shimfida a kasar - Goni
Za a zabi shugaba Buhari a 2019 ko don ayyukan da ya shimfida a kasar - Goni
Asali: UGC

Ta kara da cewa kungiyar na kan shirye shirye na buga littafi dauke da dalilai 150 da suka tabbatar da cancantar Buhari na smaun damar yin tazarce a zaben 2019, duk da cewa ta bayyana damuwarta kan yadda rikici ke ballewa a wasu sassa na jam'iyyar APC, musamman a matakan jihohi.

Goni ta ce duk da tana farin ciki da irin salon shugabancin jam'iyyar karkashin Comrade Adams Oshiomhole, ya zamarwa shuwagabannin jam'iyyar dole su shawo kan matsalolin cikin gida da jam'iyyar ke fuskanta musamman da ake fuskantar zabukan fitar da gwani.

"Jam'iyyar APC gida ne da ya hada kan kowa, bai kamata a samu rabuwar kawuna ba, sannan ya kamata a duba batun yawan 'yan takarar kujerar gwamamnan jihar Borno karkashin jam'iyyar, idan da hali a kafa kwamiti da zai sulhunta tsakanin masu neman takarar kujerar," a cewar ta.

Haka zalika ta kara jaddada bukatar shuwagabannin jam'iyyar da su sanya baki akan rikicin da ke faruwa a jihar Imo tsakanin gwamnan jihar Rochas Okorocha da kuma tsohon mataimakinsa Osita Izunaso da ma Ifeanyi Ararumi, tsohon sakataren gudanarwa na jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel