Ni zan kasance shugaban Kasar Najeriya a 2019 - Kwankwaso

Ni zan kasance shugaban Kasar Najeriya a 2019 - Kwankwaso

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma daya daga cikin manema tikitin takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa shi zai kasance shugaban kasar nan ta Najeriya a 2019.

Kwankwaso wanda a halin yanzu shine Sanatan Kano ta Tsakiya ya yi wannan furuci ne yayin da ya ziyarci jihar Filato domin neman goyon bayan wakilan jam'iyyarsa ta PDP kan kudirin da ya sanya a gaba.

Ziyarar da Kwankwaso ya kai hedikwatar jam'iyyar dake birnin Jos a ranar Alhamis ta yau, ya nemi goyon bayan wakilan jam'iyyar a yayin da zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa ke ci gaba da karatowa da za a gudanar a watan gobe.

Ni zan kasance shugaban Kasar Najeriya a 2019 - Kwankwaso
Ni zan kasance shugaban Kasar Najeriya a 2019 - Kwankwaso
Asali: UGC

Cikin barkwanci kamar yadda tsohon Gwamnan na jihar Kano ya saba, Kwankwaso ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar ta Filato, Damishi Sango, ya yi watsi da halartar wani taro na jam'iyyar da za a gudanar a birnin Abuja domin samun dama ta tarbar sa inda ya tura mataimakinsa a matsayin wakili.

Sanatan Kano yake cewa, "ni na san ba bu inda zaka gusa ko nan da can domin kuwa Rabi'u Kwankwaso ya nufato jihar Filato, da ya sanya kayi watsi da wani taro a birnin Abuja kuma ka tura Mataimakin ka a matsayin wakili domin rashin muhimmancin taron kuma ka tsaya domin yiwa shugaban kasar Najeriya na gaba lale maraba."

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya za ta yi nasara akan yakar cin hanci da rashawa - Buhari

Kwankwaso wanda tsohon Ministan tsaro ne a yayin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa yana da duk wata cancanta ta yin fito na fito da kuma zube ban kwarya da shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta gaza ta fuskar inganta harkokin ilimi da kuma samar da aikin yi ga Matasa gami da harkokin ci gaban gine-gine.

Tsohon Gwamnan na jihar Kano ya kuma sha alwashin jajircewa da tsayuwar daka wajen kawo karshen rikicin Makiyaya da Manoma a kasar nan muddin ya yi nasara a babban zaben na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel