Da zaman banza gara aikin kishiya: Tsabagen gardama ta kai wasu matasa ga kirga buhun gero

Da zaman banza gara aikin kishiya: Tsabagen gardama ta kai wasu matasa ga kirga buhun gero

Wasu matasan karamar hukumar Yawuri ta jahar Kebbi dake Arewa maso yammacin Najeriya sun dukufa wajen kirga adadin kwayar gero dake cikin buhun gero guda daya don kashe wata zazzafar musu data kaure a tsakaninsu, kamar gidan rediyon muryar Amurka ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito musu ne ya kaure a tsakanin matasan akan wai tsakanin buhun gero da al’ummar jama’an dake kasar Najeriya wanene yafi yawa, anan ne fa aka ja layi, wasu ne ganin jama’an Najeriya sun fi yawa, wasu kuma suka ce a’a buhun gero yafi yawa.

KU KARANTA: Toh fa! Malaman da El-Rufai ya sallama daga aiki sun gabatar masa da Al-kunuti

Da zaman banza gara aikin kishiya: Tsabagen gardama ta kai wasu matasa ga kirga buhun gero
Matasan
Asali: Facebook

Ana cikin haka ne sai wani yace shi ya dauki nauyin samar da buhun gero don a samu wadanda zasu kirga don tabbatar da gaskiyar adadin gero dake cikin buhu, sai a gwadashi da yawan yan Najeriya d alkalumma suka ce an kai miliyan 180.

Shugaban majalisar shan shayi da hira inda wannan musu ya kaure, Ahmad Sarkin Yaki ya tabbatar da wannan lamari, ind yace a yanzu haka sun kwashe watanni biyu suna kidayar adadin geron dake cikin buhu guda.

Da zaman banza gara aikin kishiya: Tsabagen gardama ta kai wasu matasa ga kirga buhun gero
Matasa
Asali: Facebook

Sai dai ra’ayi ya bambamta a tsakanin jama’a game da wannan aiki da bahaushe keyi ma karin magana da cewa “Da zaman banza gara aikin kishiya.” Inda wasu ke ganin kidayar a matsayin shiririta, wasu kuma ke ganinsa kamar wani biciken kimiyya.

Wani masani, kuma hakimin unguwar, kuma sarkin yakin Yawuri, Garba Alhaji Labbo ya bayyana cewa akwai dansa a cikin matasan, kuma ya basu kwarin gwiwa duk da dai baya ya dauka shirmensu kawai suke yi.

Sai dai shugaban majalisar yace kokada bawai basu da aikin yi bane, inda yace da dama daga cikinsu ma’aikatan gwamnati ne, wasu kuma yan kasuwa ne, har ma akwai masu sana’o’I fiye da daya inji shi.

Daga karshe shugaban majalisar ya bayyana cewa zuwa yanzu da dama daga cikin masu ganin jama’a Najeriya sun fi yawa sun saki tun ma kafin a kammala binciken, sa’annan yace ba zasu bayyana sakamakon bincikennasu ba har sai sun kammala kidayan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng