Zaben fitar da dan takarar PDP: Ko a kai taron Fatakwal ko na gurgunta PDP – Gwamna Wike

Zaben fitar da dan takarar PDP: Ko a kai taron Fatakwal ko na gurgunta PDP – Gwamna Wike

- Sa-in-sa ta barke a jam’iyyar PDP a kan wurin da ya kamata jam’iyyar ta gudanar da zaben fitar da dan takarar ta na shugaban kasa

- Tuni wasu daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar ta PDP suka bayyana rashin amincewarsu da yunkurin kai zaben fitar da dan rakarar Fatakwal

- Sai dai gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, ya yi barazanar gurgunta jam’iyyar ta PDP tare da saka kafar wando daya da duk dan takarar dake adawa da yin taron a Fatakwal

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi kurarin cewar zai yiwa jam’iyyar PDP lahani idan har adawar wasu ‘yan takarar shugaban kasa ta sa aka fasa gudanar da zaben fitar da ‘yan takara a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Gwamnan ya bayyana cewar duk dan takarar shugaban kasar dake adawa da gudanar da taron gangamin jam’iyyar PDP a Fatakwal dan bakincikin cigaban tattalin arzikin jihar Ribas ne kuma ba zai taba goya masa baya ba.

Zaben fitar da dan takarar PDP: Ko a kai taron Fatakwal ko na gurgunta PDP – Gwamna Wike
Gwamna Nyesom Wike
Asali: Depositphotos

Wike na wadannan kalamai ne a jawabinsa na karbar dan takarar shugaban kasa kuma gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, yayin ziyarar da ya kai jihar Ribas domin neman goyon bayan ‘ya’yan jam’iyyar PDP a cigaba da rangadin jihohin Najeriya da yake yi domin gaisuwa tare da rokon iri.

DUBA WANNAN: An kama mutumin dake yiwa Atiku da iyalinsa barazanar raba su da duniya

Duk dan takarar dake adawa da yin taron gangamin PDP a jihar Ribas ba zai samu goyon bayan wakilan jam’iyyar daga jihar ba.

“Bari na fito baro-baro na fada ma kowa ya ji, zan kwancewa PDP zani a kasuwa matukar ba a yi taron gangamin jam’iyyar a Fatakwal ba,” a kalaman gwamna Wike.

A baya jam'iyyar PDP na gudanar da taronta na gangami irin wannan ne a birnin tarayya, Abuja, kasancewar nan ne shelkwatar jam'iyyar na yake.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng