An cafke masu garkuwa da Mutane 15 a jihar Sakkwato

An cafke masu garkuwa da Mutane 15 a jihar Sakkwato

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta jihar Sakkwato ta cafke wasu miyagun 'yan ta'adda 15 da suka shahara da garkuwa da mutane, satar dabbobi da kuma fashi da makami.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Cordelia Nwawe, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai cikin birnin na Shehu a ranar yau ta Laraba.

DSP Nwawe ya bayyana cewa, an cafke wannan mutane bisa aikata miyagun laifuka na ta'addanci musamman garkuwa da mutane a kauyan Tulluwa dake karamar hukumar Rabah ta jihar.

An cafke masu garkuwa da Mutane 15 a jihar Sakkwato
An cafke masu garkuwa da Mutane 15 a jihar Sakkwato
Asali: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan 'yan ta'adda sun kuma shiga hannun hukumar bisa shahara kan aikata laifuka na fashi da makami da kuma satar shanu da suke ta'azzarar al'ummar kauyukan Tabani da kuma Tudun Dalo.

KARANTA KUMA: Yadda 'Kudan Zuma ke kawar da ƙwayoyin cututtuka masu kassara Lafiyar 'Dan Adam

Kazalika hukumar 'yan sandan ta cafke wasu 'yan ta'adda biyar a garin Bum dake karamar hukumar Wurno, bisa zarginsu kan aikata laifuka na barazanar tayar da zaune tsaye tare da kuma haddasa rikici.

Mista Nwawe ya kara da cewa, hukumar 'yan sandan ta samu wannan gagarumar nasara ne a yayin da take ci gaba da tsarkake jihar daga miyagun 'yan ta'dda bisa umarni na kwamishinan 'yan sandan ta, Mista Murtala Sani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel