Mataimakin Gwamnan Nasarawa da wasu ‘Yan takara sun fara kuka kafin zaben fitar da gwani

Mataimakin Gwamnan Nasarawa da wasu ‘Yan takara sun fara kuka kafin zaben fitar da gwani

Mun samu labari dazu cewa akalla mutum 9 cikin 11 da su ka fito takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa sun nun cewa ba za amince da kokarin da ake yi na yin coge a zaben da za ayi kwanan nan ba.

Mataimakin Gwamnan Nasarawa da wasu ‘Yan takara sun fara kuka kafin zaben fitar da gwani
Mai Girma Gwamnan Nasarawa Tanko Al-makura zai bar karagar mulki
Asali: Twitter

‘Yan takarar APC sun ce ana kokarin a sauya sunayen wadanda za su fitar da ‘dan takarar Gwamna a Jihar. Mataimakin Gwamnan Jihar Silas Ali Agara ya bayyanawa manema labarai wannan bayan sun yi wani taro a Garin Akwanga.

Sauran masu neman kujerar Gwamna a 2019 irin su Ahmed Wadada, Alhaji Danladi Envuluanza, Zakari Idde, Dauda Kigbu, Muhammed Maikaya, da Dr. James Angbazo duk sun nuna cewa ba za su amince da abin da ake kitsawa ba.

KU KARANTA:

Sauran wadanda su ke harin kujerar Gwamna mai shirin barin gado Umar Tanko Almakura irin su Shehu Tukur sa kuma Mataimakin sa Silas Ali Agara sun bayyana cewa akwai yunkurin da ake yi na murde zabe kuma ba za ta sabu ba.

Silas Agara bai bayyana wadanda su ke kokarin murde zaben tsaida ‘Dan takarar APC ba amma ya nuna cewa wasu manya a Gwamnatin Jihar na kokarin kakabawa Talakawan Nasarawa ‘Dan takarar da ba su so a zabe mai zuwa na 2019.

Envuluanza wanda yana cikin masu neman kujerar Gwamna yace idan APC ba ta dinke wannan baraka ba lallai Jam’iyyar za ta iya shan kashi a 2019. ‘Dan takarar yace dole ayi wa kowa adalci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel