NYSC: Wai a shekaru 45 dinnan kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?

NYSC: Wai a shekaru 45 dinnan kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?

- An kirkiro hukumar ne domin hadin kan yan kasa

- Zamu iya zama masu mabambantan yare, amma kasar mu daya

- A yanzu dai wannan kishin kasar babu shi

NYSC: Wai a shekaru 45 dinnan kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?
NYSC: Wai a shekaru 45 dinnan kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?
Asali: Facebook

An kirkiro da NYSC ne a Najeriya a shekarar 1973. Amfanin hukumar shine hadin kan a kasar nan tamu mai mabambantan al'adu, yarika, addinai da sauran su. Amma koda wadannan bambance bambancen, kasar mu daya ce kusan fiye da rabin karni da muka samu yancin kanmu.

An samu wasu kalubale bayan hadin kan da Lord Lugard yayi mana a 1914. Duk da bambancin mu, amma aka hada mu a kasa daya, wannan ne silar kawo kalubale da dama.

NYSC an shirya ta ne domin matasan da suka gama manyan makarantun gaba da sakandare a kasashen ketare ko a nan gida Najeriya, matukar dai suna amsa sunan su na yan kasa.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya zarce kawai, samarin kasar nan

Yan makarantu sun dau hakan a matsayin wata hanya ta sabawa da juna tare da gano yanayin rayuwar wasu al'adu da yarika a cikin fadin kasar nan. Zaka iya ganin dalibi daga jami'ar Benin an kaishi kano bautar kasa, ko daga Zaria a tura shi Ihiala dake jihar Anambra.

Shekara daya ce ta wajibci dole yayi ta domin kawo gudummawar shi ga kasar shi. Domin samun matsuguni kuwa a koina, dole ne ya nuna shaidar shi ta bautar kasa.

Amma yanzu rashin kishin kasa yasa matasa da yawa basa yin bautar kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel