Yadda 'Kudan Zuma ke kawar da ƙwayoyin cututtuka masu kassara Lafiyar 'Dan Adam

Yadda 'Kudan Zuma ke kawar da ƙwayoyin cututtuka masu kassara Lafiyar 'Dan Adam

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, binciken kwararrun masana na kiwon lafiya ya bankado wata sabuwar hanyar amfani da dafi na kudan zuma wajen warkar da miyagun ƙwayoyin cututtuka masu karya garkuwar jiki.

Wani kwararren masanin kiwon lafiya na jami'ar Dar es Salam dake can kasar Tanzania, Dakta Mkabwa Manoko, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai bayan halartar wani babban taro kan harkokin kiwon lafiya da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Duk da cewa ba boyeyyen abu bane ana amfani da ruwan Zuma wajen warkar da rauni, wani sabon bincike ya kuma bayyana yadda za a iya amfani da dafin kudan zuma wajen yakar kwayoyi na wasu miyagun cututtuka masu kassara garkuwar jiki ta lafiyar Bil Adama.

Yadda 'Kudan Zuma ke kawar da ƙwayoyin cututtuka masu kassara Lafiyar 'Dan Adam
Yadda 'Kudan Zuma ke kawar da ƙwayoyin cututtuka masu kassara Lafiyar 'Dan Adam
Asali: Depositphotos

Dakta Manoko ya bayyana cewa, kudan zuma yana fidda wani dafi da akan iya amfani da shi sakamakon karfin ikonsa wajen yakar wasu kwayoyin cututtuka masu karya garkuwar jiki irin su cutar kanjamau.

KARANTA KUMA: APC ta yiwa Dogara wankin Babban Bargo a jihar Bauchi

A sanadiyar haka kwararren likitan ya yi kira ga gwamnatocin Afirka akan su mike tsaye wajen wajen horas da al'ummominsu da kuma masana kimiya akan harkokin kiwon kudan Zuma domin tatsar wannan tabarraki da ya kunsa.

Manoko ya kara da cewa, akwai kimanin mutane miliyan biyu masu kiwon kudan zuma baya ga cibiyoyi da dama na gudanar da bincike akan kudan zuma gami da jami'o'i masu horaswa kan kiwon wannan kwari masu fa'idar gaske.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel