Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna

Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya dauki takardan takaran kujeran gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP domin kalubalantan surukin shugabansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Jaridar Daily Nigerian ta samu rahoton cewa Farfesa Hafiz ya sayi Fam din ne a sakatariya jam’iyyar PDP dake Abuja yau Laraba, 25 ga watan Satumba.

A karshen makon da ya gabata, Sanata Kwankwaso ya daga hannun tsohon kwamishanan ayyukan jihar Kano kuma Surukinsa, Abba Kabir Yusuf, a matsayin dan takaran gwamnan jam’iyyar daya tilo.

Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna
Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna
Asali: Twitter

Yayi hakan ne saboda a tunaninsa Farfesa Hafiz Abubakar da Salihu Takai basu cancanci kujeran gwamnan jihar Kano ba a yanzu, sai dai na majalisa.

Wata majiya na kusa da Farfesa Abubakar ya bayyana cewa tsohon mataimakin gwamnan ya siya takardan takaran gwamnan ne domin fito-na-fito da Kwankwaso kan maganarsa cewa basu cancanta ba.

KU KARANTA: Ni na dauko Ganduje na daura kan mulki a Jihar Kano - Inji Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar bazata birnin jihar Kano a jiya Litinin, 24 ga watan Satumba inda ya gabatar da jawabi ga mabiyansa gidansa da ke Milla Road.

Kwankwaso ya bayyana cewa dalilin zuwansa jihar Kano shine kwantar da kuran zaben sirikinsa matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP.

Kwanakin nan, tsohon gwamnan ya zabi surukansa uku. Ya zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin zabinsa a shekarar 2019. Amma Kwankwaso yace su kwantar da hankalinsu.

Ya baayyana cewa ya zabi Abba Kabir Yusuf ne saboda shine yayi zanen dukkan gadojin da akayi jihar Kano musamman na Kofar Nasarawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel