Babban jigon PDP a Katsina, Tata ya sauya sheka

Babban jigon PDP a Katsina, Tata ya sauya sheka

Yan sa’o’i kadan bayan jam’iyyar PDP a jihar Katsina ta dauki Sanata Yakubu Lado a matsayin dan takararta na kujerar gwamna, daya daga cikin yan takara masu fafutuka, Abdullahi Umar Tsauri wanda aka fi sani da Tata ya bar jam’iyyar.

A jiya Talata, 25 ga watan Satumba Tata yayi zargin cewa “kudi ya sauya hannaye” sannan kuma ya zargi jami’an jam’iyyar da son zuciya inda yace hakan ne ya tursasa shi yanke shawarar barin PDP.

A ranar Litinin, Sanata Lado ya doke sauran yan takara shida wajen samun tikin PDP a zaben gwaji da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar wanda shugabanni da mambobi daga kananan hukumomi 34 na jihar suka gudanar.

Babban jigon PDP a Katsina, Tata ya sauya sheka
Babban jigon PDP a Katsina, Tata ya sauya sheka
Asali: Depositphotos

“Zan bar PDP har abada. Tsawon shekaru inda shaye abubuwan dake faruwa a jam’iyyar musamman daga shugabannin.

“Duk da tarin alfanu da aka basu, na gano a karshe cewa babu son cigaban mutane a zukatansu sai aljihunsu,” inji shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu manyan jiga-jigai a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kokarin ganin an hana duk dan takara dake fuskantar tuhuma ko wani laifin ta’addanci daga wakiltan jam’iyyar a matsayin dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Saraki na gab da tafiya kurkuku idan bai yi wasa ba – Kungiyar Buhari tayi gargadi

Wani tsohon mamba na kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP, wanda ya nemi a boye sunansa saboda ba’a bashi izinin yin Magana kan lamarin ba ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar tsayar dad an takara da baida wata tuhuma a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel