Aisha Buhari ta bayyana dalilin kame Dogarin ta

Aisha Buhari ta bayyana dalilin kame Dogarin ta

Mun samu cewa a ranar Talatar da gabata ne uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta bayyana cewa ko kadan ba ta da hannu cikin kame babban Dogarin ta, Sani Baban-Inna, sai dai ta bayar da dalilin aukuwar wannan lamari.

Aisha Buhari ta bayyana cewa an cafke babban Dogarin ta bisa zarginsa da aikata laifi na karbar dukiya daga hannun wasu fitattun Mutane a kasar nan da sunanta.

Kamar yadda rahotanni da sanadin shafin jaridar The Punch suka ruwaito, tuni hukumar tsaro ta DSS ta dadume Baban-Inna inda a halin yanzu take ci gaba da fuskantar bincike da hukumar ke aiwatarwa a kansa.

Cikin wata sanarwa da kakakin uwargidan shugaban kasar ya bayyana, Suleiman Haruna, ya bayyana cewa Baban-Inna ya shiga hannun hukumar ta 'yan sanda bisa zarginsa da amfani da mukamin sa wajen zambace wasu mutane ta yaudararsu wajen karbe dukiyoyin su.

Aisha Buhari ta bayyana dalilin kame Dogarin ta
Aisha Buhari ta bayyana dalilin kame Dogarin ta
Asali: Depositphotos

Uwargidan shugaban kasar wadda a halin yanzu na can kasar Amurka tare da Maigidanta inda suke halartar taron majalisar dinkin duniya ta bayyana mamakin ta kwarai da aniyya, dangane da wannan zargi kan Dogarin ta da ke shafa mata bakin fenti ba tare da masaniyar ta ba a wurin wasu al'ummar kasar nan.

KARANTA KUMA: Ni zan yi nasara a Zaben 2019 - Tambuwal ya gargadi Shugaba Buhari

Kazalika Uwargidan shugaban kasar ta umurci hukumomin tsaro da wannan zargi ya shafa akan su gaggauta gudanar da bincike na diddigi domin kwato duk wata dukiya da Dogarin ta ya karba ta haramtacciyar hanya tare da ramawa Kura aniyarta.

Legit.ng ta fahimci cewa, Baban-Inna ya kasancewa babban Dogari na uwargidan shugaban kasar tun a shekarar 2016 da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel