Shekaru 3 da Buhari yayi yana mulki yafi shekaru 16 da PDP tayi nesa ba kusa ba - Minista

Shekaru 3 da Buhari yayi yana mulki yafi shekaru 16 da PDP tayi nesa ba kusa ba - Minista

- Ministan harkokin Niger Delta, Usani Usani ya jinjinawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari

- Usani ya ce shekaru uku da Buhari yayi kan mulki ya fi 16 da PDP tayi

- Ya kuma bayyana irin tarin ayyukan ci gaba da gwamnatin APC tayi a yankin Niger Delta

Ministan harkokin Niger Delta, Usani Usani a jiya Talata, 25 ga watan Satumba ya tashi don kare Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana cewa shekaru uku da yayi a kan kujerar mulki a matsayin shugaban kasa yafi shekaru 16 da PDP tayi tana mulki nesa ba kusa ba.

Usani ya fadi hakan ne yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan mika wani ginin taro da rijiyar tukaa-tuka mai aiki da hasken rana ga al’umman Ishibori na karamar hukumar Ogoja dake Cross River.

Shekaru 3 da Buhari yayi yana mulki yafi shekaru 16 da PDP tayi nesa ba kusa ba - Minista
Shekaru 3 da Buhari yayi yana mulki yafi shekaru 16 da PDP tayi nesa ba kusa ba - Minista
Asali: Twitter

Ya kara da cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da gagarumin gudun mawa wajen inganta rayuwar mutanen Niger Delta ta fannin ababen mora rayuwa da sauransu.

Ministan wanda ya yabama gwamnatin Buhari ya ci gaba da cewa, shekaru uku da shugaban kasar yayi a mulki ya samu tarin nasarori fiye da wanda PDP ta samu a tsawon shekaru 16 da ta kwashe tana mulki.

KU KARANTA KUMA: Sake zaben Osun: Omisore ya hadu da Oshiomhole, gwamnonin APC, ya amince da yiwa jam’iyya mai mulki aiki

A nasu bangaren, al'umman yankin sun nuna farin ciki da jin dadin ayyukan ci gaba da Shugaba Buhari yayi masu.

Sun kara da cewa sun shafe shekaru 30 suna neman a cika masu wannan buri nasu amma aka yi burus da lamarinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel