Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Teneo Intelligence, wata cibiyar bincike mai zaman kanta a garin New York na kasar Amurka ta bayyana cewar zaben gwamnan jihar Osun na ranar Asabar ya nuna cewar shugaba Buhari zai iya faduwa zaben shekarar 2019.

A sakamakon binciken cibiyar da jaridar Bloomberg ta wallafa, Teneo ta bayyana cewar amma idan jam'iyyar APC ta hada kan 'ya'yanta tare da dinke barakar dake cikinta, to zasu kai ga nasara.

"Sakamakon zaben Osun ba kankanuwar illa gare shi ga tasirin takarar Buhari a 2019 ba. Akwai sako cikin abinda ya faru a zaben gwamnan jihar Osun. Jam'iyyar PDP ta hada kan 'ya'yanta, kuma 'yar manuniya ta nuna cewar idan za a yi zabe na gaskiya kamar na jihar Osun, APC zata yi shan kaye a zaben shekarar 2019," a cewar Malte Liewerscheidt na cibiyar bincike ta Teneo.

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka
Buhari da Fam dinsa na takara
Asali: Depositphotos

Ko a kwanakin baya saida wani banki, HSBC, mai rassa a kasashen duniya ya yi hasashen cewar shugaba Buhari zai iya shan kasa a zaben shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Akwai damuwa: 'Yan majalisar dokoki 9 a jihar APC sun fita daga jam'iyyar

Sai dai kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu, ya yi kaca-kaca da rahoton bankin tare da bayyana cewar suna jin haushin daukewar kudin sata da ya saba kwararowa cikin bankinsu ne kawai.

Garba Shehu ya bayyana cewar bankin na HSBC na da hannu dumu-dumu cikin fitar da kudaden Najeriya da aka sace zuwa kasashen ketare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel