Babu hannu na a kamun babban dogari na – Aisha Buhari

Babu hannu na a kamun babban dogari na – Aisha Buhari

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta nesanta kanta daga rahotanni dake yawo a kafafen yada labarai cewar ta bayar da umarnin tsare sarkin dogaranta (ADC), Sani Baban-Inna, bisa zargin yin amfani da sunanta wajen karbar cin hancin biliyan N2.5 daga hannun ‘yan siyasa da jami'an gwamnati.

Sai dai Aisha ta bayyana rashin jin dadinta bisa yadda babban dogarin nata, mai mukamin Safuritanda na ‘yan sanda, ke amfani da mukaminsa da kuma kusancinta da shi wajen zambatar mutane, musamman ‘yan siyasa da jami’an gwamnati. Baban-Inna ya kasance babban dogarin Aisha tun shekarar 2016.

A jawabin da darektanta na yada labarai, Suleiman Haruna, ya fitar yau, Talata, a Abuja, Aisha ta bayyana cewar kamun da jami’an tsaro suka yiwa Baban-Inna na cikin aikinsu da doka ta tanada.

A dazu da rana ne Legit.ng da ragowar kafafen yada labarai a Najeriya suka wallafa rahoton cewar Hajiya Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muammadu Buhari, ta bayar da umarni a tsare babban dogarin ta, sannan a bincike shi akan zargin cin amanarta da yayi, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Babu hannu na a kamun babban dogari na – Aisha Buhari
Aisha Buhari
Asali: Facebook

Wannan kudi dai kamar yadda rahotanni suka bayyana kudi ne masu yawa domin sun kai kimanin naira biliyan N2.5bn.

Aisha na zargin dogarin nata ne da karbar kudade daga hannun ‘yan siyasa da jami'an gwamnati da sunan kyauta gare ta.

DUBA WANNAN: Cin hanci: ICPC ta gurfanar da Masari a gaban kotu

Babban Dogarin nata mai suna Sani Baba-Inna ya musanta karbar wadannan kudade da Aisha ke zargin sa da yin sama da fadi da su.

Aisha ta umarci sufeton ‘yan sanda, Ibrahim Idris, da ya gaggauta gudanar da bincike a kan laifin da take zargin Baban-Inna da aikatawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel