Uwargidar Atiku Abubakar ta bayyana cewa bata taba satar kudin gwamnati ba

Uwargidar Atiku Abubakar ta bayyana cewa bata taba satar kudin gwamnati ba

Uwargidar tsohon mataimakin shugban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, Titi Abubakar ya bayyana cewa ita kam bata taba satar kudin gwamnati ba wajen tafiyar da cibiyarta ta yaki da bautar da mata da kananan yara, WOTCLEF.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Titi ta bayyana haka ne a yayin taron tattaunawa a tsakanin kabilu wanda wata kungiya mai zaman kanta, cibiyar sadarwa ta Africa Media Network ta shirya a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Babbar jami’a mafi inganci a Duniya ta nada gwamnan jahar Kaduna muhimmin mukami

Uwargidar Atiku Abubakar ta bayyana cewa bata taba satar kudin gwamnati ba
Titi Atiku
Asali: Depositphotos

Titi tace a lokacin da suke gwamnati ta taimaka ma mata da kananan yara da dama da ake kokarin safararsu don bautar dasu ta hanyar tilasta musu zama karuwai, aikatau da sauransu.

“Amma ban yi amfani da kudin gwamnati ba wajen kulawa da yarannan, abinda na san anyi kawai shine gwamnati ne ta ciyar dasu abincinta. Haka zalika na dauki nauyin kudurori a majalsar dokokin kasarnan da suka zama dokoki daban daban duk don a magance matsalar safarar mutane.” Inji ta.

Titi ta cigaba da cewa: “Na kwashe tsawon shekaru 20 ina yaki da safarar mutane, kuma kimanin shekaru 30 da suka gabata na tsiri ra’ayin kare mata da kananan yara, ni tsohuwar malama ce a kwalejin kmiyya da fasa na gwamnatin tarayya dake Kaduna, kuma na yi mu’amala da dama da mata, anan na samu wannan tunani.

“Su mutanen dake safarar yaran sun sha zuwa suna min dadin baki akan na saki yaran, wai sun fi jin dadi da walwala a hannunsu fiye da yadda suke a hannuna, zuwa yanzu na ceto yaran sama da dubu goma da dari shida, kuma wasu daga cikinsu sun kammala karatun digiri.” Inji ta.

Ita ma wata shugaban kungiyar rajin kare hakkokin kananan yara da mata daga kasar Ghana, Uwargida Obaapa Awindor ta tabbatar da cewa matsalar safarar mutane ba farau bane a Najeriya, kuma be kebanta da kasar kadai ba.

Sai dai Awindor ta danganta safarar mutanen Afirka zuwa kasashen Turai ga bakin talauci da yayi mana katutu, wanda a haka ake mayar da mata karuwai, don haka ta yaba ma kafafen sadarwar zamani inda ake tattauna batun safarar mutane tare da tona asirin masu aikatawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel