Samarin Najeriya sunce shugaba Buhari ya zarce a badi, sun bada goyon baya

Samarin Najeriya sunce shugaba Buhari ya zarce a badi, sun bada goyon baya

- Matasa sun goyi bayan zarcewa Buhari

- Yakamata zabe mai zuwa ya kafa tarihi a Najeriya

- Najeriya ta dogara ne da arzikin man fetur

Samarin Najeriya sunce shugaba Buhari ya zarce a badi, sun bada goyon baya
Samarin Najeriya sunce shugaba Buhari ya zarce a badi, sun bada goyon baya
Asali: Facebook

A lokacin da zaben 2019 ke matsowa, matasan Najeriya karkashin inuwar kungiyar cigaban matasa wato Youth Progressive Association for Peace and Development, YPAD, a ranar talata ta nuna goyon bayan ta domin zarcewar mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar na kasa, Honorabul Fidelis Oryina Audu, ya bayyanawa manema labarai tareda kiran hukumar zabe mai zaman kanta da ta dage don ganin an kafa tarihi mai kyau a zabe mai gabatowa.

Kamar yanda ya fada, YPAD na kokarin aiki tare da Gwamnatin tarayya gurin kawo karshen rashawa a Najeriya.

Yace hanyoyin da sojojin Najeriya sukayi amfani dasu gurin yaki da ta'addanci zai dau lokaci Idan ba'a hada da kungiyoyin farar hula ba, balle matasa.

DUBA WANNAN: An rabe kai a kwankwasiyya

"Muna gano cewa Najeriya ta dogara ne da man fetur wanda bashi da tabbas, kwamitin zababbu na kasa ta fito da taswirar fadada tattalin arziki domin kawo hanyoyin samar da arziki abin dogaro" Yace.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel