Uwargida ta sheke diyar Kishiyar ta da maganin 'Kwari a jihar Neja

Uwargida ta sheke diyar Kishiyar ta da maganin 'Kwari a jihar Neja

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, wata matashiyar uwargida mai shekaru 20 a duniya, Zulac Kabiru, ta amsa laifinta na sheke jaririyar kishiyar ta har lahiya 'yar watanni takwas da haihuwa, Rukaiya Kabiru.

Guguwar kishi da ta debi wannan matashiya kamar yadda ta zayyana dalilin wannan aika-aika ta bayyana cewa, ta sheke jaririyar ne ta hanyar gwagwuda mata maganin kashe kwari na Fiya-fiya domin ta ladabtar da mahifiyarta akan girmama na gaba da ita.

A halin yanzu dai wannan shu'uma ta shiga hannun hukumar 'yan sanda bisa aikata laifin kisan kai a kauyen Danauta dake karamar hukumar Mariga a jihar ta Neja.

A yayin ci gaba da baje dalilan wannan ta'addanci da ta aikata, Zulac ta bayyana cewa ta yanke wannan hukunci ne domin ladabtar da abokiyar zamanta da a cewar ta ta saba cin zarafinta da kuma zagi na kare dangi.

Uwargida ta sheke diyar Kishiyar ta da maganin 'Kwari a jihar Neja
Uwargida ta sheke diyar Kishiyar ta da maganin 'Kwari a jihar Neja
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa, Zulac ta aikata wannan mummunan lamari yayin da ta silale da jaririyar inda ta kadaita da ita a wajen da ta tittila ma ta maganin na fiya-fiya da ya yi sanadiyar salwantar rayuwar ta.

KARANTA KUMA: Gwamna Bindow ya bayyana abinda sake zabensa zai haifar a jihar Adamawa

Kazalika Zulac ta kuma bayyana cewa, ta aikata wannan laifi ne a bisa sharri na Shaidan da ya yi mata busa cikin kunnenta dangane da wannan mugun nufi.

A yayin ganawarsa da manema labarai kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Muhammad Abubakar ya bayyana cewa, za a gurfanar da Zulac gaban Kuliya manta Sabo domin zartar da hukunci da ya dace gwargwadon laifi da ta aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel