Babbar jami’a mafi inganci a Duniya ta nada gwamnan jahar Kaduna muhimmin mukami

Babbar jami’a mafi inganci a Duniya ta nada gwamnan jahar Kaduna muhimmin mukami

Baban jami’ar Duniya mafi inganci kuma jami'a ta biyu da tafi dadewa a Duniya, Oxford ta sanar da nadin gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin guda daga cikin mambobin kwamitin koli, watau iyayen cibiyarta na yankin nahiyar Afirka.

Legit.ng ta ruwaito jami’ar Oxford za ta rantsar da wannan kwamitin mai dauke da mutane Tara da zai dinga bata shawara akan yadda za ta gudanar tare da tafiyar da cibiya ta Afirka a ranar 12 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Buhari ya amince da biyan naira biliyan 22 hakkokin tsofaffin ma’aikatan kamfanin jiragen Najeriya

Babbar jami’a mafi inganci a Duniya ta nada gwamnan jahar Kaduna muhimmin mukami
Jami'ar Oxford
Asali: Depositphotos

Aikin wannan kwamiti shine daura cibiyar akan tsare tsare daban daban da kuma kulla kyakkyawar alaka tsakaninta da gwamnatocin kasashen Afirka, cibiyoyi da kuma yan kasuwa da kasuwancin Afirka. Haka zalika ana sa ran mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne zai kaddamar da wannan kwamiti.

Jami’ar ta nada Tito Mboweni, bakar fata na farko daya fara shugabantar babban bankin kasar Afirka ta kudu, kuma tsohon ministan kwadago a zamanin mulkin Nelson Mandela a matsayin shugaban kwamitin, sauran yayan kwamitin sun hada da:

Gwamna Nasir El-Rufai

Alex Duncan, daga kasar Birtaniya

Ivor Agyeman-Duah, daga kasar Ghana

Ministan harkokin kasashen wajen Najeriya.

Uwargidar shugaban kasar Namibia, Madame Monica Geingos

Gareth Ackerman, shugaban kamfanin Pick’n Pay daga kasar Afirka ta kudu

Dakta Charlotte Harland-Scott, uwargidar tsohuwar shugaban kasar Zambia

Farfesa Ibrahim Gambari, tsohon mataimakin sakataren majalisar dinkin duniya

Linda Mabhena-Olagunju, shugaban kamfanin DLO Energy Group (Pty) Ltd, daga kasar Afirka ta kudu

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel