Ruwan sama kamar da bakin kwarya yaci wani babban fasto da matarsa

Ruwan sama kamar da bakin kwarya yaci wani babban fasto da matarsa

Babban jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta kasa reshen jahar Imo, Evans Ugoh ya tabbatar da mutuwar wani babban limamin addinin kirista da uwargidarsa a wani mummunan ambaliyan ruwa da aka samu a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Evans ya tabbatar da mutuwar mamatan ne a ranar Talata, inda yace an samu wannan amlabiya ne a garin Oguta na cikin karamar hukumar Oguta, sai dai bai bayyana sunayen mamatan ba.

KU KARANTA: Aiki ga mai kareka: Babban sufetan Yansanda ye nemi izinin yin binciken kwakwaf akan Lawal Daura

Amma Evans yace an samu wannan balahira ne sakamakon yin watsi da gargadin da hukumar ta bayar ga mutanen dake wannan yanki, inda yace hukumar ta umarci duk mazaunan yankin dasu tashi su bar garin don gudun irin haka, amma suka yi kunnen uwar shegu.

“A lokacin da muka gano ruwan tafkin daya ratsa garin Oguta na kara karuwa, sai muka umarci al’ummomin garuruwa bakwai dasu tattara su tashi daga yankunan don gudun ambaliya, wasu sun tashi wasu kuma basu tashi ba, sai ga shi bayan kwana bakwai ruwan ya kashe Faston da matarsa.” Inji shi.

A nasa jawabin, sarkin Oguta, Eze Nani Nzeribe ya shaida ma majiyarmu cewa sun dade suna fama da matsalar ambaliyan ruwa a wannan yanki nasu, ya kara da cewa ma’auratan sun mutu ne a yayin da suke kokarin kwaso wasu daga cikin amfanin gonakinsu.

“Bayan ruwan ya mamaye duk wasu gonakai da gidajen mutane dake garin, shine sai Faston da matarsa suka yi kokarin kwaso wasu daga cikin amfanin gonansu, amma bayan fitowarsu sai kwale kwalen dake dauke dasu ya kifa sakamakon nauyin da suka yi masa, a nan take suka mutu.” Inji Sarkin.

Daga karshe yayi kira ga hukumar NEMA da gwamnatin tarayya dasu taimaka su kaima al’ummarsa dauki, tare da daukan matakan hana faruwar lamarin a gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng