Hafsan rundunar sojin kasa TY Buratai ya gargadi jami'an soji daga sa hannu a harkokin siyasa

Hafsan rundunar sojin kasa TY Buratai ya gargadi jami'an soji daga sa hannu a harkokin siyasa

- Laftanal Janar Tukur Buratai ya gargadi jami'an soji da su kauracewa sa hannu a harkokin siyasa ko su yi murabus

-Ya tunatar da jami'an sojin da cewar an horas da su ne kan dakile duk wani aika-aika da zai kawo rabuwar kawuna, hadin kai ko zaman lafiyar kasar

- Ya bayyana cewa rundunar soji ta kaddamar shirin atisayen 'Farmakin karshe' a yankin Arewa maso Gabas don kawo karshen Boko Haram

A ci gaba da fuskantar zaben 2019, Hafsan rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai ya gargadi jami'an soji da su kauracewa sa hannu a harkokin siyasa ko su yi murabus a kashin kansu don zama cikakkun yan siyasar idan har jakan su ke so.

Da ya ke jawabi a ranar Talata a taron jami'an soji karo na 2 da na 3 da aka hada a lokaci daya a Abuja, ya ce rundunar sojin ba za ta lamunci duk wani nauyin tsoma hannun jami'i a cikin harkokin siyasa ba, illa dai kawai tabbatar da doka da oda a yayin zaben dama bayansa.

Ya tunatar da jami'an sojin da cewar an horas da su ne akan dakile duk wani aika-aika da zai kawo rabuwar kawuna, hadin kai da kuma zaman lafiyar kasar, don haka duk jami'in da aka samu yana sanya hannu a wani lamarin daban zai fuskanci hukunci.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin tarayya za ta sayar da kamfanoni 10 na kasar don samun kudin kasafin 2018

Hafsan rundunar sojin kasa TY Buratai ya gargadi jami'an soji daga sa hannu a harkokin siyasa
Hafsan rundunar sojin kasa TY Buratai ya gargadi jami'an soji daga sa hannu a harkokin siyasa
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa rundunar soji ta kaddamar da wani atisayen 'Farmakin karshe' a yankin Arewa maso Gabas don kawo karshen Boko Haram gaba daya daga yankin tafkin Chadi da kuma kokarin ganin cewa jama'ar da ta'addancin Boko Haram ya dai-daita sun koma gidajensu.

Dangane da matsalolin da ke shafar atisaye da shirye shiryen rundunar soji a kasar, musamman ma bangaren shirin Lafiya Dole, Buratai ya ce shugaba Buhari ya bada tabbacin kawo daukin gaggawa ga bukatun kawo gyara a bangaren jami'an sojin kasar.

A cewar sa, wannan sabon shirin atisayen da suke yi a sassa daba daban na kasar, zai kawo karshe mayakan Boko Haram, rikicin manoma da makiyaya, yan bindiga, satar shanu, garkuwa da mutane, lalata bututn mai da kuma yin sojin gona da sunan rundunar sojin da dai sauransu, wanda tuni aka fara samun gagarumar nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel