Siyasar Gombe: Masu jiran gwamna da kuma kujerar CBN da za'a iya baiwa Dankwambo a APC

Siyasar Gombe: Masu jiran gwamna da kuma kujerar CBN da za'a iya baiwa Dankwambo a APC

- Qishin qishin na nuna ana zawarcin gwamnan Gombe zuwa ga APC

- Watakil ayi masa gwamnan babban bankin Najeriya

- Su waye masu jiran gado a jihar?

Siyasar Gombe: Masu jiran gwamna da kuma kujerar CBN da za'a iya baiwa Dankwambo a APC
Siyasar Gombe: Masu jiran gwamna da kuma kujerar CBN da za'a iya baiwa Dankwambo a APC
Asali: Original

Rahotannin bayan fage, na nuna akwai kiraye-kiraye da ake a boye tsakanin gwamnan Gombe mai takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam'iyyar PDP, daga mai mulki ta APC, inda ake masa alkawarin idan ya zo, kujerar gwamnan CBN za'a bashi.

Dama dai daga aikin babban akanta janar ya tafi jiharsa yin gwamna, shekaru kusan goma da suka shude, inda kuma aka tabbatar yayi aiki mai kyau da tsafta, wasu kuma ke ganin a nan ne ya jaa kaaya har ya sami kudin takarar gwamna.

Koma dai menene, an san APC a yanzu tana zawarcin manyan PDP, inda itaa PDPn bata zauna nan ba, tana ta amsar wadanda aka gallazawa a jam'iyyar ta APC tun bayan cin zabe aa 2015.

DUBA WANNAN: "Zan sauke manyan hafsoshin soji"

Ba'a dai san ko Gwamna Dankwambon zai amince da wannan kira ba, watakil sai bayan ya kara da masu neman kujerar takarar a gefe a watan gobe a zabukan cikin gida na PDP. Idan ya fadi, akwai yiwuwar yace ba'a yi adalci ba, ya tafi APCn ya amshe kujerar da tai ta gwamna a jiha karfi a bayan zabukan 2019.

A gefe daya kuma, masu neman jiran gado a jihar tasa, sun zage damtse wajen suma suga sun rafto mai kyau, koda kuwa a wacce jam'iyya ce.

A jam'iyyar PDP akwai; Bala Bello Tinka, Jamilu Isiaku Gwmna, Hassan Muhammad, Dr. Mohammed Isa Wade, Abubakar Walama, Inuwa (Janjasco), Bayero Nafada, Umar Bello da Haruna Garba.

A APC kuwa akwai; Abubakar Habu Muazu, Farouk Bamusa, Ibrahim Dasuki Jalo Waziri, Inuwa Yahaya, Jibrin Danbarde, Umaru Kwairanga, Abdullahi Idris Umar da Ahmed Khamisu Mailantarki.

Ance Abuja dai, Alhaji Musa Umar Farooq take yi daga cikin masu nema a APC, inda shi kuma gwamnan aka ce yaqi fitowa fili ya nuna wanda yake yi ya zuwa yanzu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel