2019: Saraki ya kebe da 'yan takarar gwamna 10 na PDP a jihar Kwara

2019: Saraki ya kebe da 'yan takarar gwamna 10 na PDP a jihar Kwara

- Shugaban majalisa Bukola Saraki ya gana da masu neman takarar gwamna 10 a jam'iyyar PDP ta jihar Kwara

- Bukola Saraki ya kira taron ne domin tabbatar da hadin kai tsakanin 'yan takarar da suka bayyana kansu a matsayin 'yan gida daya

- Daya daga cikin 'yan takarar, Shaaba Lafiagi ya ce dukkansu 'yan gida daya kuma za su goyi bayan duk wanda ya yi nasara

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa kuma shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya gana da masu neman takarar gwamnan Kwara 10 da ke jam'iyyar PDP domin cimma matsaya kan yada za'a zaben fidda gwani cikin lafiya a ranar Lahadi mai zuwa.

Saraki ya gana da 'yan takarar gwamnan ne a gidansa da ke Ilorin a daren jiya Litinin misalin karfe 10.20 na dare zuwa 11.05 na dare in 'yan takara 9 cikin masu neman takarar 10 suka samu ikon hallarta.

Saraki ya yi ganawar sirri da 'yan takarar gwamna a jihar Kwara
Saraki ya yi ganawar sirri da 'yan takarar gwamna a jihar Kwara
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Dan takarar APC a Kwara ya tona asirin cin hancin da Saraki ya yi masa alkawari idan ya bi shi PDP

Wadanda suka samu hallartan taron sun hada da Alhaji Mohammed Ajia Ibrahim, Senator Shaaba Lafiagi, Alhaji Ladi Hassan, Mallam Bolaji Abdulahi, Hon. Razaq Atunwa, Hon. Ahman Pategi, Dr. Ali Ahmad, Alhaji Saka Isau (SAN), Professor Sulyman Abubakar amma Hon. Zakari Mohammed bai hallarci taron ba.

Sauran wadanda suka hallarci taron sun hada da mataimakin gwamnan jihar, Chief Joel Ogundeji, yayin da Ciyaman din PDP na jihar, Alhaji Kola Shittu da Sakataren jam'iyyar Alhaji Abdukrazaq Lawal suka iso gab da za'a kammala taron.

A yayin da ya ke magana da manema labarai bayan kammala taron, Lafiagi ya ce an kira taron ne domin tabbatar da hadin kai tsakanin 'yan gida daya kuma dukkan 'yan takarar sun amince za su tabbatar anyi zaben fidda gwanin cikin lumana da zaman lafiya.

Lafiagi ya kuma ce akwai yiwuwar 'yan takarar za su iya sake zaunawa domin su zabi daya daga cikinsu ya zama dan takarar jam'iyyar amma dai a yanzu ba'a dauki wannan matakin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel