Ambaliyar ruwa ya lalata gonar shinkafa mallakar Garba Shehu a jihar Jigawa

Ambaliyar ruwa ya lalata gonar shinkafa mallakar Garba Shehu a jihar Jigawa

- Ambaliyar ruwa ya lalata gonar shinkafa mallakar kakakin shugaban kasa Garba Shehu a jihar Jigawa

- An gano Garba Shehu tsaye a gaban gonar wanda ruwa ya malale ta baki daya

Ambaliyar ruwa a ya addabi jihohin kasar da dama ya lalata wani gonar shinkafa mallakar babban hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafofin watsa labarai, Garba Shehu.

Ambaliyar ruwa ya lalata gonar shinkafa mallakar Garba Shehu a jihar Jigawa
Ambaliyar ruwa ya lalata gonar shinkafa mallakar Garba Shehu a jihar Jigawa
Asali: Twitter

A ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, Garba Shehu ya yada wasu hotuna na gonarsa dake Hadejia, jihar Jigawa, wanda a cewarsa ambaliyar ruwa yayi masa ta’adi.

A hotunan da aka yada an gano hadimin shugaban kasar tsaye a wani fili dake kewaye da ruwa.

Ambaliyar ruwa ya lalata gonar shinkafa mallakar Garba Shehu a jihar Jigawa
Ambaliyar ruwa ya lalata gonar shinkafa mallakar Garba Shehu a jihar Jigawa
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta halarci taron matan shugabannin Afrika (hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da harkokin ma'adanan ruwa da binciken su watau Nigeria Hydrological Services Agency, NIHSA a takaice a ranar Alhamis din da ta gabata ta zayyana cewa kananan hukumomi 380 ne a cikin jahohi 35 za su fuskancin ambaliyar ruwa a daminar bana.

Kamar dai yadda muka samu, hukumar ta Nigeria Hydrological Services Agency ta kuma bayyana cewa akalla kananan hukumomi 78 ne za su fuskanci matsalar ambaliyar sosai fiye da sauran.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel