Zargin yi ma PDP leken asiri: Wasu ne ke yi ma Sheriff bita da kulli - Kungiya

Zargin yi ma PDP leken asiri: Wasu ne ke yi ma Sheriff bita da kulli - Kungiya

- Kungiyar magoya bayan Shugaba Buhari na 2019 sun kare shugabansu, Ali Mod Sheriff daga tuhuma

- Tsohon kwamishinan bayanai na jihar Borno dai ya zargi Sheriff da yima PDP leken asiri

- Kungiyar tace an nada Sheriff a matsayin shugaban kungiyar PDG ne sakamakon sadaukarwa da yayi wajen ganin Shugaba Buhari ya yi nasara a zabe mai zuwa

Kungiyar magoya bayan Shugaba Buhari na 2019 sun bayyana cewa zargin da ake yiwa shugaban su, Sanata Ali Modu Sheriff na cewa yana yiwa jam’iyyar adawa ta PDP leken asiri don ganin ya bata damar jam’iyya mai mulki na cin zaben 2019 ba komai bane face makirci.

Sakataren kungiyar, Hon. Kassim Muhammed Kassim a wata sanarwa da ya saki a jiya Litinin, 24 ga watan Satumba yace zargin da tsohon kwamishinan bayanai na Borno, Inuwa Bwala ke yi ba komai bane face yaudara don bata wadanda ke kokarin ganin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cimma nasarar yin tazarce.

Zargin yi ma PDP leken asiri: Wasu ne ke yi ma Sheriff bita da kulli - Kungiya
Zargin yi ma PDP leken asiri: Wasu ne ke yi ma Sheriff bita da kulli - Kungiya
Asali: Facebook

Yace an nada Sheriff a matsayin shugaban kungiyar PDG ne sakamakon sadaukarwa da yayi wajen ganin Shugaba Buhari ya yi nasara a zabe mai zuwa.

Yace Sheriff ya gamsu ne da mutunci da tsarin mulkin shugaban kasar shiyasa ya mara masa baya, sabanin zargin da ake masa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike yayi kira ga yan Najeriya da suyi aiki da hankali wajen fatattakan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga kan mulki a 2019.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta halarci taron matan shugabannin Afrika (hotuna)

Wike yace gwamnatin APC bata tabuka wani abun arziki ba kuma ta gaza cika alkawaran zaben da ta dauka.

Da yake Magana a gidan gwamnatin Jihar Port Harcourt a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, Wike yace ya zama dole yan Najeriya su hada kai wajen tabbatar da cewar APC ta sha kaye a zaben shekara mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel