Abinda ya kai Kwankwaso Kano jiya
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar bazata birnin jihar Kano a jiya Litinin, 24 ga watan Satumba inda ya gabatar da jawabi ga mabiyansa gidansa da ke Milla Road.
Kwankwaso ya bayyana cewa dalilin zuwansa jihar Kano shine kwantar da kuran zaben sirikinsa matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP.
Kwanakin nan, tsohon gwamnan ya zabi surukansa uku. Ya zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin zabinsa a shekarar 2019. Amma Kwankwaso yace su kwantar da hankalinsu.
Ya baayyana cewa ya zabi Abba Kabir Yusuf ne saboda shine yayi zanen dukkan gadojin da akayi jihar Kano musamman na Kofar Nasarawa.
KU KARANTA: Tashin hankali, Mai ya karewa Jirgin sama dauke da Sule Lamido, Shehu Sani a sama
Yace: “Na zo Kano ne domin mika godiyata na irin goyon bayan da kuka nuna mana a matsayin mambobin Kwankwasiyyaa. Ko shakka babu, zamu tattauna kan abubuwa da dama.”
“A yau, yawancin ayyukan da Ganduje ke yi jabu ne kuma akwia ha’inci a ciki, alhalin an kashe makudan kudi akansu. Amma ayyukanmu da Abba Kabir Yusuf yayi har yanzu suna nan da karfinsu a jihar Kano.”

Asali: Facebook
Kwankwaso bai dade a birnin Kano bay a koma Abuja amma yayi alkawarin dawowa cikin makonni masu zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng