'Yan sanda sun kai mamaya gidan shugaban riko na jam'iyyar PDP, jihar Kano
- 'Yan sanda sun kai mamaya gidan shugaban riko na jam'iyyar PDP, jihar Kano
- Sun je ne domin su hana shi gudanar ta taron da ya shirya
- Sun ce umurnin kotun jihar ne suka dabbaka
Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kano mun samu cewa sun kai wata mamaya a gidan shugaban kwamitin riko na jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano ranar Litinin din da ta gabata, 24 ga watan Satumba.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Gwamnan Osun ya fadi ta cikin sa bayan sakamakon zabe ya fita
Su dai 'yan sandan kamar yadda muka samu, sun je gidan shugaban rikon ne dake a kan titin Sokoto dake garin na Kano inda suka tarwatsa 'ya'yan kwamitin da sauran magoya bayan jam'iyyar ta PDP a jihar Kano dake shirin gudanar da wani taro.
Legit.ng ta samu haka zalika cewa 'yan sandan dai sun yi hakan ne domin tabbatar da umurnin babbar kotun jihar da a baya ta yanke hukunci game da takaddamar shugabancin jam'iyyar a karshen watan jiya a Agusta.
Mai karatu dai zai tuna cewa a watan jiya ne kotun ta yanke hukuncin cewa kwamitin rikon da uwar jam'iyyar PDP ta nada a jihar Kano din haramtacce ne.
A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya shirya tsaf tomin yafewa wani tsohon gwamnan tsohuwar jihar Bendel yanzu kuma jahohin Edo da Delta a Najeriya, Farfesa Ambrose Alli da aka zarga da hadame kudaden al'ummar jihar.
Mun samu cewa a lokacin mulkin shugaba Buhari na farko yana soja a shekarar 1983, wata kotu ta yankewa tsohon gwamnan wanda tuni ya mutu hukuncin dauri a gidan yari na shekaru 100 saboda samun sa da laifin karkatar da kudin yin wata hanya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng