Dambarwar 2019: Ciyamomi 21, Kansiloli 226 sun juya ma wani gwamnan Arewa baya
Kungiyar tsofaffin mataimakan shuwagabannin kananan hukumomin jahar Adamawa da kungiyar zababbun kansilolin mazabun kananan hukumomin jahar sun juya ma gwamnan jahar Adamawa baya, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyoyi sun sanar da janye goyon bayannasu ga Gwamna Jibrilla Bindow ne a wani taron manema labaru da suka kira, inda suka ce sun yi haka ne sakamakon gazawarsa wajen biyan hakkokinsu.
KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya kammala shirin daukan sabbin malaman asibiti 3,059 a Kaduna
A yayin wannan taro daya gudana a ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba, shugaban kungiyar tsofaffin mataimakan shuwagabannin kananan hukumomin, Sunday Dedan ya bayyana cewa sun janye goyon bayansu ga Bindow ne saboda gazawarsa wajen biyan akbashin ma’aikata.
Sunday yace a yanzu haka ma’aikatan kiwon lafiya, ma’aikatan muhalli har ma da ma’aikatan kananan hukumomin jahar na bin gwamnatin jahar Adamawa bashin albashin watanni takwas.
Haka zalika kungiyar tace gwamnatin jahar ta watsar dasu a matsayinsu nay an siyasa masu jama’a, don haka ne suka yanke shawarar juya masa baya tare da rungumar wani dan takarar gwamnan jahar a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
“Kamar yadda Gwamna Bindow ya saba yaudara, yayi sha yin alkawarin biyan kudin alawus na sa kaya ga tsofaffin mataimakan shuwagabannin kananan hukumomi, Sakatarori, kansiloli, da mashawarta, amma har yanzu shiru muke ji.
“Da wannan da kuma matsalolin gwamnana da suka shafi rashin cika alkawurra na gwamnan yasa mun janye goyon bayanmu a garesa, kuma muna kira ga sauran yan takarkarun gwamna a jam’iyyar APC dasu yi gaggawar zuwa su ceci jahar, musamman Dakta Mahmood Halilu Ahmed.” Inji su.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng