Sanata Mohammed Abba-Aji ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Sanata Mohammed Abba-Aji ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

- Mohammed Abba-Aji yace matsalolin cikin gida dake damun APC a jihar ne ya sanya shi ficewa daga jam’iyyar

- Yace gwamnonin APC sun yi karfi sosai hart a kai suna sanya shugabannin jam’iyyu yin ra’ayinsu

Wani dan takarar kujeran gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Mohammed Abba-Aji ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda tsarin zaren fidda gwani na wakilai da jam’iyyar ta zabi yi a jihar.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa a yanzu Abba-Aji na neman takarar kujeran sanata na Borno ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP.

Sanata Mohammed Abba-Aji ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
Sanata Mohammed Abba-Aji ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
Asali: Depositphotos

Dan siyasan yace matsalolin cikin gida dake damun APC a jihar ne ya sanya shi ficewa daga jam’iyyar.

Abba-Aji yace gwamnonin APC sun yi karfi sosai hart a kai suna sanya shugabannin jam’iyyu yin ra’ayinsu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tambuwal ya isa sakatariyar PDP domin a tantance shi (hotuna)

Ya kuma caccaki tsarin zaben fidda gwani na wakilai da jam’iyyar babin Borno tayi cewa hakan ya sabama hukuncin kwamitin masu ruwa da tsaki na APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel