Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya yayinda yan fashi suka sace mutane 7 a Zamfara

Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya yayinda yan fashi suka sace mutane 7 a Zamfara

Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Bungudu, Alhaji Hamisu Coordinator ya tsallake rijiya da baya daga hannun masu garkuwa da mutane a ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba, yayinda yan bindiga suka kai farmaki kauyen Nahuche sannan suka sace mutane bakwai ciki harda tsohon kansila, Bello Daniya.

Rundunar yan sandan Zamfara sunce yan fashin sun sace mutane bakwai a kauyen Nahuche dake karamar hukumar Bungudu.

Wani idon shaida, Malam Sani Ibrahim ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa yan fashin sun kai farmaki kauyen su da yawa, sannan suka fara harba bindigogi a sama inda suka umurci mazauna kauyen da su nuna masu gidan shugaban karamar hukumar Bungudu wanda ya kasaance dan APC.

Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya yayinda yan fashi suka sace mutane 7 a Zamfara
Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya yayinda yan fashi suka sace mutane 7 a Zamfara
Asali: Depositphotos

Ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun samu kansu a gidan tsohon kansilan, wanda ya kasance makwabcin shugaban APC, inda suka tafi dashi, da maza hudu da kuma mata biyu.

Ibrahim ya bayyana cewa daga bisani yan fashin sun saki daya daga cikin mutanen da wasika inda suka bukaci a basu naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa domin sakin sauran mutanen.

KU KARANTA KUMA: Ban yi danasanin bautawa Najeriya a karkashin Jonathan ba – Sambo

Yayinda yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu yace tawagar jami’an tsaro na bibiyar sahun masu garkuwan.

Ya roki jama’a da su sanar da hukumomin tsaro bayanai masu amfani akan duk wani motsi na masu laifi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel