Ina satar baburan mutane duk lokacin da na bukaci kudin kashewa - Gimba

Ina satar baburan mutane duk lokacin da na bukaci kudin kashewa - Gimba

- 'Yan sanda sun kama wani matashi da ya dade yana satar babura a jihar Niger

- Matashin ya ce yana satar baburan mutane ne duk lokacin da ya bukaci kudin kashewa

- Hukumar 'yan sanda ta ce za'a gurfanar da shi gaban kotu bayan an kamalla bincike

Wani barawon babur mai shekaru 24, Manyan Gimba da aka kama ya ce ya na satar ne duk lokacin da ya rasa kudin kashewa da zai amfani da shi ya biya bukatunsa na yau da kullum.

Jami'an yan sandan Najeriya reshen jihar Niger sun kama Gimba da babur kirar Bajaj wanda aka kiyasta kudin ta a N230,000.

Ina satan baburan mutane duk lokacin da na bukaci kudin kashewa - Gimba
Ina satan baburan mutane duk lokacin da na bukaci kudin kashewa - Gimba
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku ya bayyana sababbin rikicin makiyaya da manoma a Benue

Gimba wanda dan asalin kauyen Angulu ne da ke karamar hukumar Katcha na jihar Niger ya ce ya kwashe shekaru biyar yana satan baburan mutane tare da abokan aikinsa a wurare daban-daban a kauyen Wodata da ke karamar hukumar Agaie.

An kama Gimba ne bayan ya sace babur din wani Idrisu da ke zaune a kauyen Wadada.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Muhammad Abubakar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya shaidawa Punch a ranar Lahadi cewa jami'an hukumar da ke yankin Agaie ne suka damke Gimba.

Abubakar ya ce jami'an sun kama Gimba da babur kirar Bajaj guda daya kuma za'a gurfanar da shi gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel