Jam’iyyar PDP ta kawo hujjojin cewar ta lashe zaben gwamnan Osun, ta koka a kan zagaye na biyu

Jam’iyyar PDP ta kawo hujjojin cewar ta lashe zaben gwamnan Osun, ta koka a kan zagaye na biyu

A yau, Lahadi, ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewar akwai bukatar komawa zagaye na biyu a zaben gwamnan jihar Osun da aka kamala jiya, Asabar.

Dalilin INEC na cewar sai an koma zagayen raba gardama shine ba zata yiwu ta bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben ba saboda adadin kuri'un da suka lalace a zaben sun fi adadin kuri'un da suka bashi rinjaye a zaben.

Wani dalili da INEC suka kara bayarwa shine cewar sai dan takara ya sami kashi 25% na biyu bisa ukun (2/3) kananan hukumomin jiharsa kafin a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Jam’iyyar APC ta samu nasara a Kananan Hukumomi 15 yayin da PDP ta lashe Kananan Hukumomi 11 kacal. ADP kuma ta samu nasara a Karamar Hukumar Iwo yayin da SDP ta kawo Kananun Hukumomin Ife ta tsakiya da Gabas.

Jam’iyyar PDP ta kawo hujjojin cewar ta lashe zaben gwamnan Osun, ta koka a kan zagaye na biyu
Dan takarar PDP, Sanata Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Sai dai jam’iyyar PDP ta fusata da wannan mataki da INEC ta dauka tare da bayyana cewar ana kokarin yi mata fashi ne da tsakar rana, kamar yadda yake a jawabin da sakatarenta na yada labarai, Kola Ologbondian ya fitar.

PDP ta kafe kan cewar dan takararta, Sanata Ademola Adeleke, ya lashe zaben bayan samun kuri’u mafi rinjaye a saboda haka ya zama wajibi hukumar INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya she zaben bisa dogaro da kwandin tsarin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 1999.

DUBA WANNAN: Ma'aikacin INEC da ya yaga sakamakon karamar hukuma ya shiga hannu, ya fadi wanda ya saka shi

Sashe na 179 (2) (a)(b) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace, ba tare da wani rudani ba, waye ya zama zakara a duk zaben da aka gudanar,” a cewar jawabin na PDP.

Sannan ta cigaba da cewa, “kamar yadda yake a kundin tsarin mulki, mun cika sharuda biyu da suke tabbatar da nasara a zaben gwamna, wadanda su ne – (a) dan takara ya samu kuri’u mafi rinjayen kuri’un da aka kada sannan (b) kada jimillar dan takarar gwamna ya gaza samunkaso 1/3 na kuri’un da aka kada a kaso 2/3 na dukkan kananan hukumomin jihar daya yi takara.”

Bisa dogaro da wannan hujjoji ne jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu, ya gaggauta janye batun zagaye na biyu tare da bayyana dan takararta a matsayin zababben gwamnan jihar Osun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel