Da dumi-dumi: Gobara a gidan Malam Ibrahim Shekarau (Bidiyo)

Da dumi-dumi: Gobara a gidan Malam Ibrahim Shekarau (Bidiyo)

Labarin da ke shigo mana yanzu daga jihar Kano na nuna cewa gidan tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, kuma dan takaran sanatan Kano ts tsakiya ya kama da wuta.

Wannan abu ya faru da yammacin yau Lahadi, 23 ga watan Satumba 2018 sanadiyar matsalar wutan lantarkin gidan. Dakuna biyu ne kawai abun ya shafa.

Mai magana da yawun Shekarau, Sule Yau, ya tabbatar da wannan labari ne ga jaridar Premium Times bayan mun wallafa tare da bidiyon.

Babu labarin cewa an samu rauni ko hallakan rayuwa, kana jama'a sun kashe wuta da wuri kafin ya harzuka.

The house was built by the Kano State Government towards the end of Mr Shekarau’s second tenure (2007-2011) as part of his severance package.

Gwamnatin jihar Kano ce ta ginawa Malam Ibrahim Shekarau wannan gida a karshen mulkinsa a shekarar 2011 matsayin la'adan bautawa al'ummar jihar,

Kalli bidiyon:

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng