Zaben Osun: Akwai yiwuwar sai an je zagaye na biyu, dalilai

Zaben Osun: Akwai yiwuwar sai an je zagaye na biyu, dalilai

A yayin da jama'a ke cigaba da jiran hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala jiya, akwai yiwuwar sai an je zagaye na biyu domin tantance waye ya lashe zaben gwamnan jihar.

Tuni dai masana doka suka kammala bayyana hujjojin a kan cewar ba zai yiwu INEC ta bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben ba saboda adadin kuri'un da suka lalace a zaben sun fi adadin kuri'u 300 da suka bashi rinjaye a zaben.

Wani dalili da masanan suka kara bayarwa shine cewar sai dan takara ya sami kashi 25% na biyu bisa ukun (2/3) kananan hukumomin jiharsa kafin a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

A baya Legit.ng ta sanar da ku cewar sakamakon Karamar Hukuma guda kadai ya rage a gane wanda zai lashe zaben Jihar Osun. Wannan Karamar Hukuma dai ita ce Osogbo inda nan ne babban Birnin Jihar Osun kuma mafi yawan Jama’a a kaf Jihar.

Zaben Osun: Akwai yiwuwar sai an je zagaye na biyu, dalilai
Akwai yiwuwar sai an je zagaye na biyu, dalilai
Asali: Original

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa da zarar an samu cikakken sakamakon Garin Osogbo za a gane wanda zai zama sabon Gwamnan Jihar Osun. Yanzu dai an kawo sakamakon kananan Hukumomi 29 cikin 30 da ake da su.

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa APC tana da kuri’u 224, 488 yayin da Jam’iyyar adawa na PDP ke da kuri’a 236, 784. Hakan na nufin PDP ta sha gaban APC da kuri’a 12, 000. Yanzu dai sakamakon Osogbo kurum ake sa rai ya fito

DUBA WANNAN: An kama jami'in INEC da ya yaga sakamakon karamar hukuma, ya fadi wanda ya saka shi

Jam’iyyar APC ta samu nasara a Kananan Hukumomi 15 yayin da PDP ta lashe Kananan Hukumomi 11 kacal. ADP kuma ta samu nasara a Karamar Hukumar Iwo yayin da SDP ta kawo Kananun Hukumomin Ife ta tsakiya da Gabas.

Yanzu haka dan takarar PDP, Sanata Ademola Adeleke, keda mafi rinajen kuri'u a sakamakon da aka kamma tattarawa duk da an hada da sakamakon zaben karamar hukumar Osogbo da ake ta jira.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel