Zaben Osun: Ma’aikacin INEC da ya yaga sakamakon zabe ya shiga hannu, ya fadi wanda ya saka shi

Zaben Osun: Ma’aikacin INEC da ya yaga sakamakon zabe ya shiga hannu, ya fadi wanda ya saka shi

Wani ma’aikacin hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Osun, Salawu Mutiu Kolawole, ya shaidawa manema labarai cewar mai gidansa ne ya saka shi yaga sakamakon zaben karamar hukumar Ayedaade a zaben gwamnan jihar da aka kamma jiya.

Tun kafin Kolawolen ya shiga hannu, dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar PDP, Mista Dele Adeleke, ya yi korafin cewar sakamakon da aka gabatar a cibiyar tattara sakamako ya sha banban da wanda aka lika a karamar hukumar Ayedaade.

Wasu ma’aikatan hukumar INEC sun gargadi Kolawole a kan yin Magana da ‘yan jarida kuma yana cikin Magana da ‘yan jaridar ne jami’an ‘yan sanda suka yi awon gaba da shi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

A wata ganawa da shugaban jam’iyyar PDP a jihar Osun, Mista Soji Adagunodo, ya shaidawa Daily trust cewar akwai yunkurin canja sakamakon nasarar da suka samu a zaben domin bawa jam’iiyar APC fifiko.

Zaben Osun: Ma’aikacin INEC da ya yaga sakamakon zabe ya shiga hannu, ya fadi wanda ya saka shi
Ma’aikacin INEC da ya yaga sakamakon zabe bayan ya shiga hannu
Asali: Original

A baya Legit.ng ta sanar da ku cewar sakamakon Karamar Hukuma guda kadai ya rage a gane wanda zai lashe zaben Jihar Osun. Wannan Karamar Hukuma dai ita ce Osogbo inda nan ne babban Birnin Jihar Osun kuma mafi yawan Jama’a a kaf Jihar.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa da zarar an samu cikakken sakamakon Garin Osogbo za a gane wanda zai zama sabon Gwamnan Jihar Osun. Yanzu dai an kawo sakamakon kananan Hukumomi 29 cikin 30 da ake da su.

DUBA WANNAN: Zaben Osun: Magoya bayan PDP sun fara rera waka suna tikar rawar murnar hango nasara (Hotuna)

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa APC tana da kuri’u 224, 488 yayin da Jam’iyyar adawa na PDP ke da kuri’a 236, 784. Hakan na nufin PDP ta sha gaban APC da kuri’a 12, 000. Yanzu dai sakamakon Osogbo kurum ake sa rai ya fito.

Jam’iyyar APC ta samu nasara a Kananan Hukumomi 15 yayin da PDP ta lashe Kananan Hukumomi 11 kacal. ADP kuma ta samu nasara a Karamar Hukumar Iwo yayin da SDP ta kawo Kananun Hukumomin Ife ta tsakiya da Gabas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel