Hangen nasara: Magoya bayan PDP sun fara rera waka suna tikar rawar murna
A jiya Asabar ne, 22 ga watan Satumba 2018, al'ummar jihar Osun suka gudanar da zaben gwamna da zai shugabancin jihar a shekaru 4 masu zuwa. Da misalin karfe 3:35 na safiyar yau, Lahadi ne hukumar INEC ta fara sanar da sakamakon zaben kowace karamar hukuma.
A kidaya na karshe, kafin shigowar sakamakon karamar hukumar Osogbo, Legit.ng ta kawo maku adadin kuri'un da kowacce jam'iyya ta samu kamar haka;
PDP
Yawan kuri'u: 254698
APC
Yawan kuri'u: 254345
SDP Yawan kuri'u:
128049
ADP
Yawan kuri'u: 49744
ADC
Yawan kuri'u: 7681
Ganin wannan sakamako ya saka masoya da magoya bayan jam'iyyar PDP da dan takarar ta fara murnar hangen samun nasara a zaben na jiya.
DUBA WANNAN: Alkiblar nasarar zaben gwamnan Osuna ta canja bayan shigowar sakamakon Osogbo
Duk da sakamakon karamar hukumar Osogbo da ake dako ya shigo hannu, ya zuwa yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ba ta fadi waye ya lashe zaben ba.
Zaben gwamnan jihar ta Osun da ya gudana a jiya Asabar, na iya zama fitilar haska zaben 2019 kamar yadda jakan kungiyar kasashen turai da ke Nigeria ya bayyana, wanda kuma zai kawo karshen mulkin Ogbeni Rauf Aregbesola na tsawon shekaru 8.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng