Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Kamar yadda wasu masana da masu hasashe suna sanar cewar tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, zai tsayar da surukinsa, Abba Kabir Yusuf, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP, hakan ta tabbata.

Kazalika Kwankwaso ya zabi tsohon kwamishininsa na harkokin cikin gida, Aminu Abdulsalam, a matsayin dan takarar mataimakin Abba K. Yusuf.

Kwankwaso, tsohon gwamna, sanata mai ci, sannan dan takarar shugaban kasa, ya kasance jagoran jam’iyyar PDP a jihar Kano kuma madugun darikar Kwankwasiyya. Ana ganin babu wani dan takara a PDP da zai yi tasiri idan ba Kwankwaso ne ya tsayar da shi ba.

Kwankwaso ya yanke shawarar tsayar da Yusuf a matsayin dan takararsa bayan wata doguwar ganawa da magoya bayansa a yau, Asabar, a Kaduna. Sanarwar tsayar da Yusuf ta fito ne a daren yau bayan kamala dogon taron.

Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP
Kwankwaso da 'yan takararsa
Asali: Twitter

A labaran Legit.ng na ranar yau, Asabar, kun ji cewar Farfesa Hafizu Abubakar, tsohon mataimakin gwamna Ganduje ya sayi fam din takarar kujeran Sanatan Kano ta tsakiya biyo bayan matsin lamba daga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

DUBA WANNAN: Abubuwa 6 da masu sa-ido a zaben Osun suka zakulo

Majiyar mu dake da kusanci da Farfesa Hafizu ta sanar da mu cewar yanzu haka Farfesan yana Kaduna wurin tantance 'yan takara. Hafizu ya yanke shawarar tsayawa takarar ne domin biyayya ga Kwankwaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel