Abun kunya: Da fitilar kwai ake amfani a wurin tattara sakamako, hoto

Abun kunya: Da fitilar kwai ake amfani a wurin tattara sakamako, hoto

A yayin da jam’ar jihar Osun suka fita domin kada kuri’unsu kuma har sakamako ya fara samuwa daga wasu mazabu daga fadin kananan hukumomi, an hango wurin tattara kuri’u na mazabar karamar hukumar Ileogbo na amfani da fitilar kwai saboda rashin wutar lantarki.

A yau ne, Asabar, 22 ga watan Satumba, 2018, masu kada kuri’a a jihar Osun zasu zabi sabon gwamna da zai maye gurbin gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, da wa’adin mulkinsa ya kare.

Bayan dukkan jam’iyyu, musamman APC mai mulki da PDP mai adawa, sun kamala yakin neman zabensu, Legit.ng ta kawo maku wasu muhimman abubuwa 7 da ya kamata ku sani dangane da zaben nay au, Asabar, 22 ga watan Satumba, 2018.

Abun kunya: Da fitilar kwai ake amfani a wurin tattara sakamako, hoto
wurin tattara sakamakon zabe
Asali: Facebook

1. ‘Yan takara 48 ne ke takarar neman maye gurbin gwamna Rauf Aregbesola mai barin gado

2. Adadin mutane 1,687,492 hukumar zabe (INEC) ta yiwa rajisatar zabe a jihar Osun

3. Adadin katin zabe 1,246,915 INEC ta raba

4. Akwai mazabu 332 a jihar Osun

DUBA WANNAN: Hafizu ya yi biyayya ga Kwankwaso, ya sayi fam din takara

5. Jihar Osun na da kananan hukumomi 30

6. Hukumar INEC ta raba na’urar tantance masu kada kuri’a guda 4,700

7. Kungiyoyin sa ido na gida da ketare zasu halarci tare da kula da sahihancin zaben

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel