Da dumin sa: Yan bindiga sun sace dan wani babban mai mukami a gwamnatin Kano

Da dumin sa: Yan bindiga sun sace dan wani babban mai mukami a gwamnatin Kano

- Yan bindiga sun sace dan wani babban mai mukami a gwamnatin Kano

- Dan shugaban karamar hukumar Kiru ne aka sace

- Sun ce sai an basu Naira miliyan 50

Shugaban karamar hukumar Kiru dake a jihar Kano mai suna Nasiru Mu'azu ya tabbatarwa da majiyar cewa wasu 'yan bindiga sun sace dan sa mai suna Babangida a ranar Larabar da ta gabata a jihar ta Kano.

Da dumin sa: Yan bindiga sun sace dan wani babban mai mukami a gwamnatin Kano
Da dumin sa: Yan bindiga sun sace dan wani babban mai mukami a gwamnatin Kano
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Wani malamin addini yayi kaca-kaca da masoyan Buhari

Shi dai Babangida din kamar yadda muka samu magidanci ne da matar sa daya da 'ya'ya biyu kuma an sace shi ne a gidan sa dake a karamar hukumar ta Kiru, jihar Kano.

Legit.ng ta samu cewa haka zalika a wani bincike da muka yi, mun samu cewa 'yan bindigar sun bukaci mahaifin na sa da ya basu Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa idan har yana so a sako shi.

Jami'an 'yan sandan jihar ta Kano ma dai sun tabbatar da aukuwar lamarin kuma sun tabbatar da cewa tuni har sun bazama aiki ka'in da na'in domin ganin sun kubutar da shi.

A wani labarin kuma, Hukumar kididdiga ta kasa watau National Bureau of Statistics, (NBS) a turance a cikin wani sabon daftarin rahoton kididdiga ta fadi yawan kudaden da ake bin kasar Najeriya da yanzu haka ke karkashin kulawar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Alkaluman da hukumar ta fitar dai sun bayyana cewa kawo yanzu ana bin Najeriya kudaden da suka kai dalar Amurka biliyan 22.08 daga kasashen waje yayin da kuma ake bin kasar Naira triliyan 3.48 daga cikin gida Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel