Hukumar kididdiga ta kasa ta fallasa yawan bashin da ake bin gwamnatin Buhari

Hukumar kididdiga ta kasa ta fallasa yawan bashin da ake bin gwamnatin Buhari

- Hukumar kididdiga ta kasa ta fallasa yawan bashin da ake bin gwamnatin Buhari

Tace dalar Amurka biliyan 22.08 ake bin Najeriya daga kasashen waje

- Sannan Naira triliyan 3.48 ake bin mu daga cikin gida Najeriya

Hukumar kididdiga ta kasa watau National Bureau of Statistics, (NBS) a turance a cikin wani sabon daftarin rahoton kididdiga ta fadi yawan kudaden da ake bin kasar Najeriya da yanzu haka ke karkashin kulawar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Hukumar kididdiga ta kasa ta fallasa yawan bashin da ake bin gwamnatin Buhari
Hukumar kididdiga ta kasa ta fallasa yawan bashin da ake bin gwamnatin Buhari
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An gano wanda Kwankwaso ke son ya gaji Ganduje

Alkaluman da hukumar ta fitar dai sun bayyana cewa kawo yanzu ana bin Najeriya kudaden da suka kai dalar Amurka biliyan 22.08 daga kasashen waje yayin da kuma ake bin kasar Naira triliyan 3.48 daga cikin gida Najeriya.

Legit.ng ta samu cewa aka zalika alkaluman kididdigar sun bayyana cewa jihar Legas ita ce tafi kowace jiha a cikin 36 da ke a kasar cin bashi yayin da kuma jihar Anambra take da mafi karancin bashin akan ta.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta sha sukar gwamnatin ta shugaba Buhari inda a lokuta da dama takan zarge ta da ciwo ma kasar bashi na babu gaira babu dalili.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya a zamanin mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana goyon bayan takarar shugancin kasar Najeriya da Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal keyi.

Babangida ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya din a ranar Asabar a gidan sa dake a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel