Zaben Gwamnan jihar Osun ya zo karshe, an fara kidayar 'Kur'iu

Zaben Gwamnan jihar Osun ya zo karshe, an fara kidayar 'Kur'iu

Za ku ji cewa wa'adin shekaru takwas kan karagar mulki na gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya karato inda al'ummar jihar sa suka yi tururuwa zuwa wajen kada kuri'unsu yayin zaben gwamnan jihar dake gudana a yau Asabar.

Ko shakka ba bu rahotanni sun bayyana cewa, an tsananta tsaro mai ingancin gaske yayin zaben gwamnan jihar dake wakana a yau Asabar 22 ga watan Satumba kamar yadda hukumar zabe ta kasa ta kayyade tun a baya.

Kai tsaye da sanadin wakilan mu dake can jihar Osun domin tatsao sahihan rahotanni, mun samu cewa a halin yanzu zaben ya zi kan gaba inda tuni an fara tantance tare da kidayar kuri'un wasu mazabu da aka riga da kammala zaben su.

Zaben Gwamnan jihar Osun ya zo karshe, an fara kidayar 'Kur'iu
Zaben Gwamnan jihar Osun ya zo karshe, an fara kidayar 'Kur'iu
Asali: Original

Rahotanni da suke zuwa mana a halin yanzu sun bayyana cewa, tun misalin karfe 2.30 na ranar yau aka fara kidayar kuri'u na mazabun wasu yankuna dake karamar hukumar Ile Ife ta Tsakiya da kuma wasu mazabun na Akarabata inda jam'iyyar SDP ta fyada sauran jam'iyyun da kasa.

KARANTA KUMA: An yi tururuwa wajen Zaben Gwamnan jihar Osun cikin tsaro mai tsanani

Legit.ng ta ruwaito cewa, ana fafata wannan zabe na kujerar gwamnan tsakanin jam'iyyu daban-daban har 48, inda dan takarar na jam'iyyar APC, Adegboyega Oyetole, Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP, Fatai Akinbade na jam'iyyar ADC, Moshood Adeoti na jam'iyyar ADP da kuma Iyiola Omisore na jam'iyyar SDP ke gaba sama da sauran jam'iyyun.

Kazalika jaridar The Punch ta ruwaito cewa, tuni dan takara na jam'iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke, ya lashe zaben mazabar sa ta Abogunde/Sagba inda ya lallasa sauran jam'iyyu da kuri'u 154.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel