Ribar Noma: Farashin Garri ya fadi warwas a kasuwannin jihar Enugu

Ribar Noma: Farashin Garri ya fadi warwas a kasuwannin jihar Enugu

- Farashin Garin kwaki na ci gaba da faduwa kasa warwas a wasu kasuwanni na jihar Enugu

- Farashin buhun Garri ya sauko kasa daga N8,000 zuwa N5,000

- Saukowar farashin na da nasaba da noma rogo da akayi a jihar sosai a wannan shekarar a jihar

Wani bincike da aka gudanar ta hanyar zagayawa kasuwanni a ranar Asabar dinnan, ya bayyana cewa farashin fari da jan garin kwaki ya sauko kasa warwas da kusan kashi 36 na kudin da ake sayar da shi a baya.

Wasu daga cikin yan kasuwa da aka zanta da su sun bayyana cewa farashin garin ya sauko ne duba da yawan manoman rogo da aka samu a fadin jihar.

Miss Eby Ofor, wacce ke sayar da garri a kasuwar Akwata, ta ce farashin boki mai cin lita 4.5 na farin garri wanda a baya ake sayar da shi N450 yanzu ya koma N280. Ta kara da cewa jan gari ana sayar da shi N350 a yanzu mai makon N550 da ake sayar da shi a baya.

"Kusan wata hudu da suka gabata, ina sayar da kwanon farin garri akan N450, sannan jan garri akan N550, amma yanzu farashin ya sauko sosai, kusan an koma sayar da shi akan rabin farshinsa na baya" a cewarta.

Ribar Noma: Farashin Garri ya fadi warwas a kasuwannin jihar Enugu
Ribar Noma: Farashin Garri ya fadi warwas a kasuwannin jihar Enugu
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: Osun 2018: Jami'an tsaro sun sake cafke jami'in PDP yana sayen kuri'u a mazabar Adeleke

Mr. Jude Ugwueze, wani dilan garri a kasuwar Garki, ya ce yanzu ana sayar da buhun garri akan N5,000 mai makon N8,000 da ake sayar da shi a baya.

Wata mai sayen garri a babbar kasuwa Ogebte, Mrs Joy Solomon ta nuna jin dadinta akan yadda farashin garin ke ci gaba da saukowa kasancewar babu kudi a hannun jama'a.

"Ko ba komai da faduwar farshin garin yanzu, dan kudin da mutum ya ke da su zai iya bashi damar ciyar da iyalansa," a cewarta.

Mr Romanus Eze, shugaban kungiyar manoman rogo, reshen jihar Enugu ya ce yawan noman rogon da aka yi a wannan shekarar ya taimaka wajen faduwar farashin garri a kasuwanni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel