Suruki ya sa an kashe mijin diyarsa, kan banbancin kabila

Suruki ya sa an kashe mijin diyarsa, kan banbancin kabila

- Mahaifina yasa aka kashe mijina

- An kashe shi har lahira a gaban matar shi

- Muna kaunar junanmu shiyasa mukayi aure

Suruki ya sa an kashe mijin diyarsa, kan banbancin kabila
Suruki ya sa an kashe mijin diyarsa, kan banbancin kabila
Asali: Depositphotos

A ranar 14 ga watan satumba ne aka kashe Pranay Perumulla a gaban matarshi, Amrutha.

Amrutha da Pranay masoya ne tun a makaranta a Miriyalaguda, wani karamin gari ne a kudancin India. Sun fara haduwa ne a makarantar gaba da sakandare.

Amrutha mai shekaru 21,asalin yar masu hannu da shuni ce, shi kuwa Pranay mai shekaru 24,dan masu karamin karfi ne. Sunyi aure a watan Afirilu 2016 duk da iyayen su basu so ba.

"Mahaifina ne yasa a kashe mijina saboda bambancin nasaba. "

Yan sanda dai sun cafke mahaifin nata, Maruti Rao da wasu mutane shida, wanda ya hada da Dan uwan Mista Rao da wasu mutane 3 da ake zargin su da kwangilar kisan.

DUBA WANNAN: Manyan dalilai da suka sa aka daina fasa bututan mai

Shugaban yan sandan yankin, AV Ranganath ya sanar da manema labarai cewa ana zargin Mista Rao da hada baki da yan'uwan shi da wasu mutane gurin halaka sirikin su. Mutane biyun sun samo mishi kwangilar masu kashe mutane a rupee miliyan 10.

Ya kara da cewa Mista Rao ya ansa laifin shi inda yace yayi hakan ne saboda sirikin nashi Dan talakawa ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel