El-Rufai, Lai sun isa jihar Osun gabannin zaben gwamna da za’a gudanar a gobe

El-Rufai, Lai sun isa jihar Osun gabannin zaben gwamna da za’a gudanar a gobe

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, da ministan labarai, Lai Mohammed, a halin yanzu suna a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Sun sauka a jihar da misalin karfe 1:00pm sannan suka nufi gidan gwamnatin Okefia, Osogbo, inda suka samu tarba daga Rauf Aregbesola, gwamnan jihar.

Gwamnonin biyu tare da Mohammmed sun halarci sallar juma’a a masallacin gidan gwamnati.

El-Rufai, Lai sun isa jihar Osun gabannin zaben gwamna da za’a gudanar a gobe
El-Rufai, Lai sun isa jihar Osun gabannin zaben gwamna da za’a gudanar a gobe
Asali: Depositphotos

Akwai rahotanni dake nuni cewa Bola Tinubu, babban jigon APCna kasa ma yana a jihar.

Gboyega Oyetola, tsohon shugaban ma’aikata ga Aregbesola, ya kasance dan takaran jam’iyyar APC mai ci.

KU KARANTA KUMA: Sabani ya shiga tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa

Akwai yan takara 48 a zaben amman tseren na a tsakanin Oyetola, Ademola Adeleke na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Iyiola Omisore na Social Democratic Party (SDP) da kuma Moshood Adeoti, na Action Democratic Party (ADP).

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan Kano kuma dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, SanataRabiu Kwankwaso, yace yana da karfin bige shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe.

Ya kuma bayyana cewa zai tabbatar da ganin an samu zaman lafiya, matakan tsaro da kuma kayan more rayuwa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben kasa na 2019.

Ya fadi haka ne a ranar Juma’a, 21 ga watan Satumba a lokacin wani hira a Channels Television, inda yayi ikirarin cewa yana da mabiya da dama da zasu sa yayi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel