Kungiyar Shia ta Labanon, Hizbulla, tace wai tanadi manyan makamai masu linzami

Kungiyar Shia ta Labanon, Hizbulla, tace wai tanadi manyan makamai masu linzami

- Iran ke aikawa rukunan Shia makamai da kudade

- Iran na so ta kafa sojoji a yankunan duniya

- Hizbolla sun fi sojojin Labanon karfi

Kungiyar Shia ta Labanon, Hizbulla, ta tanadi manyan makamai masu linzami
Kungiyar Shia ta Labanon, Hizbulla, ta tanadi manyan makamai masu linzami
Asali: UGC

Kungiyar yaki da sunkuru ta 'yan shi'a mai zama a kasar Labanon watau Hizbullah, wadda take karkashin jagorancin Hassan Nasrallah, mai kokarin ganin ya karar da Yahudawa a duniya, tace duk da matsin kasar Israila, a yanzu ta sami makaman zamani.

Ita dai kungiyar, tana kokarin ganin ta kafa kasar Falastinu ne a yankin da Yahudawa ke zama, wadanda suka kwata suka mamaye shekaru 70 da suka wuce.

Kasar Iran ce ke baiwa yaranta makamai, da kudade, a kasashe masu tasowa, inda akan sami wadannan kungiyoyi su fi gwamnati karfi.

Misali, kungiyar Hizbolla tafi gwamnati da sojojinta karfi a kasar Labanon, mai makwabtaka da Jordan da Saudiyya.

DUBA WANNAN: An kashe rai a zanga-zagar Shia

Haka ma a Yemen, kasar Iran ta baiwa 'yan shiar Houthi makamai, inda suka kori gwamnati suka tumbuke shugaban kasar, wanda ya kai har yau ana yaki da Saudiyya a kasar.

Makaman da Iran din ke aikawa, suna rikita kasashe ne inda masu tada kayar bayan, kance ai babu wata gwamnati sai tasu kuma su kwace wa kowa 'yanci.

Shugaban kungiyar Hezbollah ta Lebanon ya ce sun samu makamai na zamani duk da kokarin Isra'ila na hana ta yin hakan. Hassan Nasrallah ya shaida wa magoya bayansa cewar kokarin Isra'ila na katse wa kungiyar hanyoyin samun makamanta ba za su yi tasiri ba.

Isra'ila dai ta sha kai hare hare ta sama a Syria da nufin kassara duk wani yunkuri na Iran wajen samar da makamai na zamani ga abokan kawancenta, wato kungiyar ta Hezbullah.

Yace: "duk wani mataki da kuka dauka na datse hanyoyin, yanzu zance ya kare, kuma kungiyarmu ta mallaki makaman roka na zamani, da wadanda ba su kai su inganci ba, dama fasahar kera sauran makamai."

Hassan Nasrallah ya ce "bakin alkalami ya bushe., idan Isra'ila ta daura damarar yaki da Lebanon, to kuwa Isra'ilar za ta fuskanci wata makoma, da wani yanayi, wanda ba ta taba zatonsa ba ko da da rana guda."

Sai kuma Amurka mai marawa Irailar bawa, wadda itace kasa kadai da larabawa suka sha yii wa taron dangi don murkushewa, har sau shida, kuma duk basu yin nasara.

A 2006 aka gwabza tsakanin Israila da Hizbolla, kuma kowanne bangare ya ji jiki, inda aka ruguje kasar tsaff, tunda ta bari 'yan shi'ar sun mamaye ko'ina da makamai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel